Zaben Gwamnan Kaduna: Ana Cigaba Da Ruɗani Yayin Da Uba Sani Ya Yi Tsokaci Ga Hukuncin Kotu
Gwamnan jihar Kaduna Uba Sani ya mayar da martani kan hukuncin da kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan jihar ta yanke ranar Alhamis.
A cewarsa, hukuncin ya fito karara na tabbatar da farin jinin da al’ummar jihar suka ba shi.
KARANTA WANNAN LABARIN: Da Ɗumi-Ɗumi: Kotu ta kori Gwamna Uba Sani, ta bayyana cewa zaben Kaduna bai kammalu ba
Sai dai jaridar DAILY POST ta rawaito cewa an samu rudani kan hukuncin da kotun ta yanke.
Yayin da wasu rahotanni ke cewa kotun ta tabbatar da zaben Sani bayan ta yi watsi da karar da jam’iyyar PDP da dan takararta Isa Ashiru suka shigar, wasu bayanai na hukuncin sun ce kotun ta tsige gwamnan yayin da ta bayyana zaben shi a matsayin wanda bai kammala ba.
Amma a martaninsa kan hukuncin, Uba ya yaba da hukuncin, yana mai cewa ya ji dadi matuka.
A cikin wata sanarwa da ya sanya wa hannu da kansa ya ce “Hukuncin na tabbatarwa ne da farin jini da amana da mutanen jihar Kaduna suka ba ni.”
“Ina yaba wa Kotun bisa tsayuwar dakan da suka nuna. Sun wadatar da haqqoqinmu da aiwatar da dimokuradiyyar zaɓe.
“Ina kuma yabawa dan uwana, Hon. Isah Ashiru Kudan saboda tunkarar Kotun domin nuna koken sa.
“Wannan ya nuna a sarari na imaninsa ga ka’idojin dimokuradiyya da kuma wajabcin wayewa a cikin halayen ‘yan siyasa.
“Ina kira ga Hon. Isah Ashiru da ‘yan jam’iyyar adawa ta jihar Kaduna da su hada hannu da mu domin kokarin ciyar da jihar mu gaba.
A wani labarin kuma:Kotu Ta Tabbatar Da Nasarar Gwamnan Kaduna
Kotun sauraren kararrakin zaben gwamna a jihar Kaduna ta tabbatar da nasarar Gwamna Sani Uba.
Da take yanke hukunci a cikin karar da jam’iyyar PDP da dan takararta, Isah Mohammed Ashiru, suka shigar domin kalubalantar nasarar Gwamna Uba Sani, kwamitin ya ce Sani ya yi daidai.