Kotun daukaka kara ta bayyana Natasha Akpoti-Uduagan a matsayin wadda ta lashe zaben Sanatan Kogi ta Tsakiya
Kotun daukaka kara ta amince da hukuncin da kotun sauraron kararrakin zabe ta yanke tunda farko a Lakwaja.
Kotun daukaka kara dake zamanta a Abuja ta tabbatar da Natasha Akpoti-Uduagan a matsayin zababbiyar sanata mai wakiltar mazabar Kogi ta tsakiya, kamar yadda gidan talabijin na Channels ta ruwaito.
Karanta nanKada Wanda Ya Sake Shigowa Taron Majalisar Zartaswa Idan Bamu Gayyace Shi Ba-Tinubu
Kotun ta yi watsi da karar da Abubakar Ohere ya shigar saboda rashin cancanta inda tace ya kasa gabatar da shaidu akan karar da ya shigar akan nasarar Natasha
A watan Satumba ne kotun sauraron kararrakin zabe ta jihar Kogi da ke zamanta a Lokoja ta soke zaben Mista Ohere na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben Sanatan Kogi ta tsakiya.
Kotun ta kara da bayyana Natasha Akpoti-Uduagan ta jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a matsayin wadda ta lashe zaben.
Sai dai Mista Ohere ya daukaka kara kan hukuncin amma kotun daukaka kara ta amince da hukuncin da kotun ta yanke na ayyana Mrs Akpoti-Uduagan a matsayin wacce ta lashe zaben.
A wani labarin KumaYanzu Lokaci Ya Yi da Zaka Kawo Karshen Burin Ka Na Neman Shugaban Kasa – Martanin Tinubu Ga Atiku
Jahar Kogi zata gudanar da zaben gwamnan jahar nan da sati daya mai zuwa inda za a gwabza tsakanin dan takarar jam’iyar APC mai samun goyon bayan gwamna Yahaya Bello da kuma Sanata Dino Melaye na jam’iyar PDP da sauran manyan ‘yan takara.