Wata kotun daukaka kara dake zamanta a Abuja a ranar Talata ta tabbatar da zaben tsofaffin gwamnonin jihar Sokoto biyu, Aminu Tambuwal da Aliyu Wamakko a matsayin sanatoci masu wakiltar Sokoto ta Kudu da Sokoto ta Arewa.
Zaben Tambuwal wanda ya kasance tsohon gwamnan jihar kuma dan takarar jam’iyyar PDP ya samu kalubalantar tsohon Sanata mai wakiltar gundumar, Ibrahim Danbaba yayin da Wamakko ya kalubalanci tsohon mataimakin gwamnan jihar, Manir Dan’ iya.
Karanta nanAn Bukaci Gwamnati Da Ta Yi Wani Abu Dangane Da Talaucin Dake Addabar ‘Yan Nijeriya
Alkalan mutum uku karkashin jagorancin Mai shari’a Mustapha Muhammad a cikin shari’o’i guda biyu, sun yi fatali da karar da Danbaba ya shigar a kan Tambuwal tare da bayar da tarar Naira 500,000 ga wadanda ake kara da kuma jam’iyyarsa ta siyasa ta PDP.
Da yake jawabi, daya daga cikin manyan lauyoyin wanda ake kara kuma na PDP, Suleiman Usman, ya ce yayin da aka amince da zaben Tambuwal, karar da tsohon mataimakinsa ya kai Wamakko ya ci tura.
Usman ya ce,kotu ta yanke hukuncin ne kan zaben Sanata guda biyu a jihar.
Yayin da kotu ta tabbatar da zaben Sanata Tambuwal, masu shari’a uku a cikin hikimar su kuma sun ci tarar N500,000 ga wanda ya shigar da kara domin goyon bayan wanda ake kara da kuma PDP.
A wani labarin kumaTsohon kwamishinan lafiya na Nasarawa Abimiku ya rasu
A halin da ake ciki, kotun kuma bisa hikimarta ta yi watsi da karar da muka shigar a madadin tsohon mataimakin gwamna, Manir Dan’iya a kan tsohon gwamna kuma Sanata mai wakiltar Sakkwato ta Arewa, Aliyu Wamakko.
Kotu ta kuma ci tarar wanda ba zan iya tunawa ba a kan wanda muke tuhuma a kan wannan shari’a.