Daga: Abbas Yakubu Yaura
Wata Kotun Majistare dake zamanta a Iyaganku Ibadan, a ranar Juma’a, ta tsare wasu masu sana’ar sayar da ganye da kuma wani mutum guda a gidan gyaran hali na Abolongo bisa zargin kashe wata mata mai suna Mudijat.
Masu maganin gargajiyar biyu sun hada da Ismail Wasiu, mai shekaru 29, da Shittu Mutairu, mai shekaru 35, yayin da dayan wanda ake kara shine Kareem Rafiu, a.k. da kuma Omo Odo Agba mai shekaru 26.
Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN ya ruwaito cewa ana tuhumar wasu mutane ukun Wasiu, Mutairu da Rafiu bisa tuhume-tuhume biyu na hada baki da kuma kisan kai.
Alkalin kotun, Misis Munirat Giwa-Babalola wadda ba ta amsa rokon wadanda ake kara ba saboda rashin hurumin shari’a, ta bayar da umarnin tsare su a gidan gyaran hali na Abolongo,dake cikin Garin Oyo.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa mai shari’a Giwa-Babalola tace za a ci gaba da tsare wadanda ake tuhumar, har sai an kammala aikawa da karar su zuwa ma’aikatar shari’a ta jihar Oyo.
Mai gabatar da kara, ASP Sunday Fatola, ta shaida wa kotun cewa wadanda ake tuhumar su uku sun hada baki ne wajen aikata laifin na kisan kai, Fatola tace: “Masu sana’ar sayar da ganyen su biyu ne suka je wurin wani yaron yahoo dake bukatar kai na mutum, yayin da Mutairu ya shirya ya yaudare wanda abin ya shafa Mujidat ‘F’ zuwa Saki daga jihar Legas.
“Wadanda ake tuhumar sun yi sanadin mutuwar Mujidat ba bisa ka’ida ba, ta hanyar yanka ta da wuka.” Inji Fatola, mutane Ukun Wasiu, Mutairu da Rafiu, sun tsinke gawarta, suka shiryata a cikin buhu kafin a kama su.
Sannan Yace an aikata laifin ne a ranar 24 ga watan Oktoba, da misalin karfe 10:00 na dare. a unguwar Ato, Ayekale, Saki ta jihar Oyo.
Fatola tace laifin ya sabawa sashe na 316 da kuma hukuncin dake karkashin sashe na 319 da 516 na kundin laifuffuka na 38, II, na Dokokin Jihar Oyo na shekarar 2000.
Mai shari’ar ta dage ci gaba da sauraron karar har zuwa ranar 12 ga watan Janairu na shekarar 2022.
Comments 1