Kotu mai lamba ta 9 dake zaune a Maitama a babban birnin tarayya Abuja ta umurci rundunar ‘yan sandan Nijeriya da su gaggauta sakin gawarwakin ‘yan’uwa Musulmi almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky, wadanda jami’an tsaron ‘yan sandan suka kashe a ranar 22 ga watan Yulin shekarar 2019 A Babbar Sakatariyar gwamnati dake Abuja biyo bayan muzaharar neman a saki jagoransu da suka yi a wannan rana.
A yayin muzaharar, an zargi hukumar ‘yan sanda da kashe mutum tara tare da raunata mutane da daman gaske, biyo bayan hakan an zargi jami’an tsaron da kwashe gawarwakin mabiya mazhabar shi’a din.
Alkalin kotu na 9 dake babban Kotun kasa, Mai Shari’a Taiwo O. Taiwo shi ne ya yanke hukuncin a saki gawarwakin tare da biyan kimanin naira miliyan biyar (5,000,000) ga kowacce gawa.
Sannan Alkalin ya bai wa Daraktocin Asibitin kasa dake Abuja da na Asokoro umurnin su yi maza su saki gawarwakin ga iyalansu.
Hakan ta faru ne yau bayan dage shari’ar da ake yi, wanda yau ya zamanto ranar karshe na jin hukunci.
Bayani sun nuna cewa ‘yan sanda ba su turo wakilansu kotun ba. Kuma ba su aiko da takardar korafi ba.