By Ishaq Dabai
Mai shari’a Abiodun Adesodun na babbar kotun Ado Ekiti ya yanke wa wasu mutane uku hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa laifin fashi da makami da kisan kai. Wadanda aka yankewa hukuncin sune Oluwole Edward mai shekaru 49, da Kolawole Ojo 39 da Kolawole Tope mai shekaru 20.
Adesodun, a cikin hukuncinsa, ya furtawa “kowanne daga cikin wadanda ake tuhuma da laifi kamar yadda ake tuhuma”.
Alkalin ya yankewa kowanne daga cikin wadanda ake tuhuma hukuncin daurin shekaru biyar ba tare da zabin biyan tara ba kuma akan laifuka biyu, na hudu, biyar da shida, mai shari’ar ya yanke musu hukuncin kisa ta hanyar rataya.Ana tuhumar mutanen uku da laifin hada baki, fashi da makami da kisan kai.
A cewar Daraktan masu gabatar da kara na jama’a, Julius Ajibare, wadanda ake tuhuma sun aikata laifin tsakanin ranar 12 ga watan Afrilu, 2017 zuwa 5 ga watan Disamba na shekarar 2017.
Sannan yace ”yayin da suke dauke da bindiga sun yi wa wadanda suka kashe fashi, Wasiu Ayinde na Naira 1,850,000 akan hanyar Erinmope-Ayedun Ekiti.”Ya shaida wa kotun cewa sun kuma yi wa Adamo Ayinde fashin kudi Naira 1,450,000 a kan hanyar Orin-Ido Ekiti; Liadhi Mukadam shima Naira 1,530,000 akan hanyar Otun Ekiti-Ilofa da Alhaji Fatai Arowolo na Naira 2,200,000 akan titin Ayedun-Omuo Ekiti.
Da yake shaida a gaban kotun, daya daga cikin wadanda abin ya rutsa dasu, yace wadanda aka yanke wa hukuncin ne suka tattara wayar sa, yace ya kai rahoton lamarin ga ofishin ‘yan sanda kuma daga baya an bibiyi wayar sannan hakan ya kai ga cafke masu laifin.
Mai gabatar da kara ya shaidawa kotun cewa wadanda ake tuhumar sun aikata laifuka na sashi na 516, 402 (2) da 319 (1) na kundin laifuka, C16, Dokokin jihar Ekiti ta Najeriya.
Kazalika ya kira shaidu biyar, baje koli, wadanda suka hada da bayanan wadanda abin ya rutsa dasu da wadanda aka yankewa hukunci, da kuma takarda da aka rubuta wa Kwamishinan ‘yan sanda, da sauran su. Wadanda aka yankewa hukuncin sun yi magana ta hanyar shawarwarin su kuma basu kira sheda ba.