Wata babbar kotun jihar Ekiti da ke zamanta a Ado Ekiti ta yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya ga wani Kazeem Olabisoye da Owolabi Usman bisa samun su da laifin hada baki da fashi da makami, da kuma daurin rai da rai a kan yunkurin aikata kisan kai.
Daily Post ta ruwaito cewa, An gurfanar da mutanen biyu da aka yanke wa hukuncin a gaban mai shari’a Adekunle Adeleye bisa tuhume-tuhume uku.
KARANTA WANNAN LABARIN: Mutane 15 Da Zasu Halarci Bikin Mauludi Sun Nutse A Teku
A cewar tuhume-tuhumen, wadanda aka yankewa hukuncin, sun yi wa wata kungiyar agaji ta Odo Charity da kuma iyalanta fashin kudi har naira ₦40,000 tare da yunkurin kashe Ugwe Ebuka ta hanyar damke shi a Ekute dake birnin Ado Ekiti.
Al’ummar dake kusa da wurin ne suka rinjayi wanda ake tuhuma a unguwar yayin da sauran abokan aika-aikan nasu suka gudu.
Tawagar masu gabatar da kara karkashin jagorancin Daraktan shigar kararrakin jama’a, na jihar Julius Ajibare, ta gabatar da shaidu hudu tare da gabatar da shaidu biyar don tabbatar da karar ba tare da wata shakka ba.
L.A. Fasanmi ya wakilci mai laifi na 1 yayin da mai laifi na 2 Adeyinka Opake ya wakilce shi.
A WANI LABARIN KUMA: Gwamna Zulum Ya Bada Umarnin Hada Koyar Da Sana’o’i A Makarantun Tsangaya Sama Da 3, 000
Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum, ya ba da umarnin hada sana’o’in hannu a makarantun Almajiri 3,226 da ke fadin jihar.
Thisday ta ruwaito cewa Zulum ya bayar da wannan umarni ne domin bullo da sana’o’i a cibiyoyin Tsangaya sama da 2,775 da kuma Makarantun Islamiyya 451 jihar ta Borno.