Akalla mutane 15 ne aka ruwaito sun rasa rayukansu bayan da jirgin ruwan da suke ciki ya kife a kan rafin da ke karamar hukumar Shagari a jihar Sokoto. Kamar yadda Daily Trust ta nakalto.
Wakilin Majiyar Dimokuradiyya ya tattaro cewa lamarin ya afku ne da yammacin ranar Talata a lokacin da wadanda abin ya shafa za su je wani kauye da ke makwabtaka da su don halartar bikin Moulud Nabiy, domin tunawa da ranar haihuwar Annabi Muhammad S.A.w.
KARANTA WANNAN LABARIN: Gwamna Zulum Ya Bada Umarnin Hada Koyar Da Sana’o’i A Makarantun Tsangaya Sama Da 3, 000
Shugaban karamar hukumar, Aliyu Abubakar Dantani, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ya ce, wadanda abin ya shafa sun fito ne daga kauyuka daban-daban.
Ya ce, “Su 25 ne a cikin jirgin ruwan lokacin da jirgin ya kife amma an ceto 10 daga cikinsu da ransu. Sun fito ne daga kauyuka hudu daban-daban, suka hadu a daya daga cikin kauyukan dake kusa da Kogin, daga nan suka shiga kwale-kwalen.
“Suna kan hanyarsu ta zuwa wani kauye domin halartar bikin Moulud na shekarar nan amma kwale-kwalen ya kife kafin su isa inda suke.
“Mutane 15 ne suka nutse amma daga baya an gano gawarwakinsu kuma aka binne su kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.”
A cewar Dantani, hudu daga cikin wadanda suka mutun, sun fito ne daga kauyen Gidan Raket, uku daga Gidan Dawa, bakwai daga Sabon Garin Sullubawa, sai kuma yarinya daya daga Tsohon Garin Sullubawa.
A kan alkawarin da Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya yi a shekarar 2021 na samar da rigunan ceto a kauyukan da ke kusa da karamar hukumar, shugaban ya ce “har yanzu ana kan jiran tsammani”
Karamar hukumar Shagari dai ta shafe shekaru tana fama da hadurran jiragen ruwa. Kuma ko a a cikin shwkarar 2021, wani jirgin ruwa ya kife da bakin daurin aure, inda mutane 13 wadanda galibi mata da yara ne suka mutu a kauyen Ginga sanadiyar lamarin.
Kazalika ko A cikin watan Afrilun bana, wasu matasa 29 ciki har da wata amarya sun mutu a hatsarin kwale-kwale a kauyen Gidan Magana da ke kusa da Kogin.
A Wani labarin kuma: Da Dumi-Dumi: Mayakan Rasha Na Tsere Daga Yankin Kherson
Dubun dubatar fararen hula da jami’an Rasha da aka nada ne ake kwashe su daga yankin Kherson na kudancin Ukraine, gabanin harin da Ukraine ke cigaba da kaiwa kansiu in ji shugaban yankin da Rasha ta nada.
Vladimir Saldo wanda shi ne Magajin Garin Kherson tun bayan karbe iko da yankin, ya ce fararen hula dubu hamsin zuwa sittin za su bar garuruwa hudu da ke yammacin gabar kogin Dnieper a wani “tsare-tsare, gudun hijira nan ba da jimawa ba”.