Tsohon gwammnan jihar Imo Rochas Okorocha ya bukaci kotu ta bayyana mamayar da hukumar EFCC ta yiwa gidansa da cewa bai kamata ba, kuma hakan ya saba da kundin tsarin mulkin kasa.
Okorocha wanda Sanata ne mai wakiltar Imo ta yamma a majalisar dattawan kasar nan, kazalika ya bukaci kotun ta tilasta a biya shi kudi naira Biliyan daya sakamakon lalata masa gida da jami’an hukumar EFCC suka yi, lokacin da suka mamaye gidansa da nufin kama shi.
Wadannan bayanai na daga cikin tarin bukatan da lauyansa Dr. Mike Ozekhome (SAN) ya gabatar gaban babbar kotun tarayya dake Abuja, wanda suka ambaci hukumar EFCC da kuma babban lauyan gwamnatin tarayya kuma ministan shari’a Abubakar Malami SAN a matsayin wadanda suke kara.
Karin lauyan Dr. Mike Ozekhome (SAN) yanzu lauyoyin dake kare Okorocha sun zama guda Biyar, kuma dukkansu masu mukamum SAN.
Jim kadan bayan wannan roko daga lauyan Okorocha sai lauyan hukumar EFCC ya bukaci kotu ta dage zaman domin gabatar da wasu shaidu masu sukar ikirarin da bangaren okorocha yayi.
A karshe mai shari’a Inyang Ekwo ya dage zaman zuwa yau domin duba kan batun bayar das hi Beli, tare da umartar ci gaba da tsare shi.
Comments 1