By Abbas Yakubu Yaura
Wata kotun kasar Myanmar a ranar Litinin ta sake dage yanke hukunci a kan shari’ar da ake yi wa Aung San Suu Kyi kan yada labarai ba bisa ka’ida ba,a cewar wata majiya da ke da masaniya kan lamarin.
Ana tsare da wadda ta samu lambar yabo ta Nobel tun bayan da sojoji suka yi juyin mulki a kan gwamnatinta a ranar 1 ga watan Fabrairu, wanda ya kawo karshen wa’adin mulkin dimokuradiyyar kasar a kudu maso gabashin Asiya.
An dai gamu da murkushe masu gudanar da zanga-zangar kin jinin gwamnati a fadin kasar, inda aka kashe mutane sama da 1,300 tare da kama sama da 11,000, a cewar wata kungiyar sa ido ta cikin gida.
Suu Kyi, mai shekaru 76, za ta saurari hukuncin ne kan tuhume-tuhumen da ake yi mata na shigo da bayanai ba bisa ka’ida ba da kuma mallakar wayoyi – na baya-bayan nan a cikin kundin shari’ar da aka yanke a wata kotun mulkin soja da ke iya ganin an daure ta har tsawon rayuwarta.
Sai dai alkalin kotun ya dage shari’ar har zuwa ranar 10 ga watan Janairu, kamar yadda wata majiya da ke da masaniya kan lamarin ta shaida wa kamfanin dillancin labaran faransa AFP, ba tare da bayar da cikakken karin bayani ba.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa A farkon wannan watan, an daure Suu Kyi na tsawon shekaru hudu saboda tunzura sojoji da keta dokar COVID 19, a wani hukunci da kasashen duniya suka yi Allah wadai da shi.
Daga baya shugabar gwamnatin Junta Min Aung Hlaing ta mayar da wa’adin zuwa shekaru biyu sannan ta ce za ta yi zamanta a gidan kaso a Naypyidaw babban birnin kasar.
Suu Kyi dai zata fuskanci zaman gidan yari na tsawon shekaru uku idan har aka same ta da laifin yada labaran kanzon kurege, wanda ya samo asali ne tun farkon juyin mulkin lokacin da sojoji da ‘yan sanda suka kai samame gidanta da ake zargin sun same ta da kayan haramcin.
Ana kuma tuhumar Suu Kyi da laifuffuka da dama na cin hanci da rashawa – kowanne daga cikinsu yana da hukuncin daurin shekaru 15 a gidan yari – da kuma karya dokar sirrin hukuma.
An hana ‘yan jarida halartar zaman kotun na musamman a Naypyidaw kuma a baya-bayan nan an dakatar da lauyoyinta daga yin magana da manema labarai.