Gwamnatin tarayya ta bukaci kungiyar kwadago ta Najeriya NLC da ta dakatar da yajin aikin gargadi na kwanaki biyu da ta ke shirin yi fadin kasar.
Simon Lalong, ministan kwadago da samar da ayyukan yi ne ya yi wannan roko yayin da ya ce ya kamata a janye yajin aikin saboda matsalar tattalin arziki da ke addabar ‘yan Najeriya.
Da yake jawabi ga manema labarai a Abuja ranar Litinin, Lalong ya bukaci kungiyar NLC da ta baiwa gwamnatin tarayya lokaci domin biyan bukatun ta.
Saboda irin wannan matakin zai yi illa ga nasarorin da aka riga aka samu a kan hanyarmu ta samar da kyakkyawar makoma ga ma’aikatan Najeriya da ‘yan kasa baki daya.
KARANTA NANBa Zan Baku Kunya Ba–Shugaba Tinubu Ga Yan Najeriya
Bugu da kari kuma, ina rokon shugabanin kungiyar NLC ta baiwa wannan gwamnati wani lokaci domin ta sasanta tare da magance matsalolin da ke faruwa a kasa baki daya.
Ya kamata a gane cewa ba da dadewa ba ne Mista Shugaban kasa ya rantsar da majalisar ministocin wannan gwamnati, kuma dukkan ‘yan majalisar sun taka rawar gani wajen karbar bayanai daga MDAs dinsu.
Saboda haka, batutuwan da shugabannin NLC suka gabatar, wasu batutuwa ne da ni da Karamin Ministan Kwadago da Aiki ake yi mana bayani a kai inji Lalong.
Lalong ya bayyana kwarin gwuiwa da yake dashi akan shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu keyi wajen ganin yan Najeriya sun samu saukin gudanae da rayuwarsu ta yau da kullum.
A WANI LABARIN KUMA
Kuyi Koyi Da Jami’an Amoetokun-Sarkin Gummi Ga Arewacin Najeriya
Mai martaba Sarkin Gummi Justice Hassan Muhammad ya bukaci mazauna Arewacin Najeriya da su tabbatar da sun yi koyi da Jami’an tsaron Amoetokun Wajen yakar rashin tsaro da ya dabaibaye yankin tsawon shekaru.