Jami’an rundunar sojin Najeriya tare da hadin gwiwar jami’an kula da kadarin Gwamnatin NSCDC sun gano wasu wuraren tace man fetu da ba bisa ka’ida ba a kalla 12.
Jaridar DIMOKURADIYYA ta tattaro cewa Sun gano wauraren ne a yankin Owahwa Creek da ke karamar hukumar Ughelli ta Kudu a jihar Delta.
Jami’an sun kuma gano tukunyar dafa abinci guda 60, da tankunan ruwa 14, da wasu jiragen ruwa na katako guda 6 makare da danyen mai na sata, da kuma galan 470 na man fetur da aka tace ba bisa ka’ida ba a sansanonin.
Wata sanarwa da Daraktan hulda da jama’a na rundunar, Burgediya Janar Onyema Nwachukwu ya bayyana cewa sojojin sun kuma kama wani danyen mai da aka sace a Udu da Tsekelewu da ke karamar hukumar Warri ta Arewa a jihar Delta.
KARANTA WANNAN Sojoji Sun Gano Wata Haramtacciyar Matatar Man Fetur A Nigeria
Sanarwar ta ci gaba da cewa, “Dakarun sojojin Najeriya tare da hadin gwiwar jami’an tsaro na Civil Defence sun ci gaba da murkushe masu zagon kasa a bangaren man fetur na Najeriya a Kudancin Najeriya.
“Dakarun Bataliya ta 181 Amphibious Battalion da ke gudanar da aikin yaki da satar mai a ranar Asabar, 2 ga watan Satumbar 2023, sun fatattaki sansanonin barayin mai da ke Owahwa Creek a karamar hukumar Ughelli ta Kudu a jihar Delta.
“A farmakin da sojojin suka kai sun gano haramtattun wuraren tace mai har guda 12, da tukhnyar dafa abinci 60, da tankunan ruwa guda 14, da kwale-kwalen katako 6 da aka sace, da buhu 470 na AGO da aka tace ba bisa ka’ida ba, da aka boye a sansanonin.
“Hakazalika, sojojin kuma sun kama wata mota dauke da buhunan polytene guda 25 da ake zargin AGO ta tace ba bisa ka’ida ba a yankin Ogbodu da ke karamar hukumar Udu ta jihar Delta.
“A wani sumame makamancin haka da aka yi a ranar 2 ga Satumbar, 2023, sojojin Bataliya ta 3, sun kama wasu kwale-kwalen katako guda biyu makare da danyen mai a Tsekelewu, da kekaramar hukumar Warri ta Arewa a jihar Delta.”
Onyema ya ce a karamar hukumar Tsekelewu, an kama wasu mutane biyu da ake zargi da laifin satar mai.
“Sojojin sun kuma kama mutane biyu da ake zargi da aikata laifin. An mika wadanda ake zargi da kuma haramtattun kayayyakin ga jami’an NSCDC da ke aikin Tsaron Tantita don ci gaba da daukar mataki.
Jaridar PUNCH ta rawaito cewa Sanarwar ta kara da cewa, “an yi kira ga jama’a da su kai rahoton duk wani aiki da ake zargi na yin zagon kasa ko aikata laifuka ne ga jami’an tsaro don inganta ayyukan da ake yi na dakile zagon kasa a kasar nan,” in ji sanarwar.
A Wani Labarin Kuma Wani Mahaifi Ya Zargi NYSC, Da Hukumomin Tsaro Da Sakaci Bayan Sace ‘Yarsa
Mahaifin wata mambar NYSC da aka yi garkuwa da ita a jihar Zamfara, ya zargi hukumomin tsaro da hukumar masu yi wa kasa hidima ta kasa da nuna ko in kula kan lamarin.
Diyar Emmanuel Etteh na daya daga cikin dalibai takwas da aka yi garkuwa da su ‘yan Uyo, a jihar Akwa Ibom zuwa sansanin su na NYSC.