Gwamnatin Najeriya ta yi kira ga kasashen da ake zargin na goyon bayan Nnamdi Kanu, da haramtaciyarsa ta ‘Yan asalin Biyafara (IPOB), da su daina.
Ministan shari’a kuma babban Lauyan Gwamnatin Tarayya, Abubakar Malami, ya ce irin wadannan kasashe na tallafa wa ayyukan Kanu, da IPOB, duk da sun kwana da sanin cewa gwamnati da ayyana kungiyar a matsayin ta ta’addanci a Najeriya.
Mista Malami wanda ya kira taron manema labarai a ofishinsa da ke Abuja a ranar Jumma’a kana daya bayan da aka gabatar da Mista Kanu don sake gurfanar da shi a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja kan tuhume-tuhume bakwai da suka shafi cin amanar kasa da ta’addanci.
Jawabin nasa ya ta’allaka ne kan rahoton binciken da kwamitin wucin gadi na shugaban kasa mai membobi 24, wanda Shugaba Muhammadu Buhari ya kaddamar, biyo bayan tsare Kanu a wajen Najeriya a watan Yuni.