Gwamnatin tarayya ta zargi gwamnonin Nijeriya da yin gasa a tsakaninsu ta fuskar adadin masu dauke da cutar Koronabairos a jihohinsu, kamar yadda Jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Wannan bayanin kamar yadda majiyarmu ta labarto ya fito ne daga bakin babban jami’i na kwamitin kar ta kwana da fadar shugaban kasa ta kafa kan cutar korona a Nijeriya, Dr. Sani Aliyu.
Dr. Aliyu ya gargadi gwamnonin da su kaurace wa takara ko kuma yin gasa a tsakaninsu ta ganin samun adadin masu cutar korona a matsayin wata hanyar yin rige-rige.