Gwamnatin jihar Oyo ta umurci duk masu rike da mukaman siyasa a wa’adin farko na Gwamna Seyi Makinde da su mayar da duk motocin da aka ware musu ba tare da bata lokaci ba.
Gwamnatin jihar ta shawarci wadanda aka sallama da su dawo da motocin a ranar Juma’a, 25 ga watan Agusta, 2023.
Gwamnatin jihar ta ba da umarnin ga tsofaffin ma’aikatan a ranar Juma’a, a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun sakataren gwamnatin jihar, Farfesa Olanike Adeyemo.
KARANTA NANRashin Ilimi Ne Ya Janyo Ma Yan Najeriya Talaucin Da Suke Ciki-Tinubu
Sanarwar ta ce Gwamna, Mataimakin Gwamna, Shugaban Majalisa da ‘Yan Majalisa, Babban Alkalin Jihar, Alkalai, Sakataren Gwamnatin Jiha, Shugaban Ma’aikata,Kwamishinoni, Sakatarorin dindindin, Akanta,Babban Auditors da Surveyor-General an keɓe su daga umarnin.
Sanarwar ta kuma kara da cewa, su wadannan mutanen da aka kebe anyi hakan ne bisa ga umarnin gwamnan.
Ya kara da cewa jami’an da ke da hujjojin da ke tabbatar da da’awar cewa an ba su kyautar motocin hukuma su gabatar da shaida don tsara jadawalin jami’ai a MDAs.
Sanarwar da aka rabawa DAILY POST ta hannun babban sakataren yada labarai na gwamnan, Sulaimon Olanrewaju, ta bukaci wadanda har yanzu suke rike da motocin gwamnati ba tare da izini ba da su dawo da su ranar Juma’a, 25 ga watan Agusta, 2023.
Ma’aikatan Jadawalin Ma’aikatu,da Hukumomi (MDAs) a Hukumar Kula da Ma’aikata ta Jiha an ba su izinin kwato motocin da aka tafi da su ba tare da izini ba, idan ba a dawo da su ba a ranar Juma’a, 25 ga Agusta, 2023.
A WANI LABARIN KUMA
Rashin Tsaro A Najeriya Na Matukar Tayar Min Da Hankali-Peter Obi
Tsohon dan takarar shugaban kasa a karkashin Jam’iyar LP a babban zaben da ya gabata Peter Obi ya bayyana cewar rashin tsaro a fadin Najeriya na matukar Tatar masa da hankali idan yaga halin