Mai Alfarma Sarkin Musulmi kuma Shugaban Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci ta Najeriya (NSCIA), Alhaji Sa’ad Abubakar III, ya umarci al’ummar Musulmi da su duba jinjirin watan Dhul-Hijja tun daga gobe Laraba.
Sarkin ya yi wannan kiran ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Farfesa Sambo Junaidu, shugaban kwamitin ba da shawara kan harkokin addini na Majalisar Sarkin Musulmi ta Sokoto.
“Wannan yana sanar da al’ummar musulmi cewa ranar Laraba 29 ga watan Yuni, daidai da 29 ga Zul-Qidah 1443AH, ita ce ranar da za a fara duba jinjirin watan Dhul-Hijjah 1443AH.”
Sanarwar ta kara da cewa, “Saboda haka an bukaci musulmi da su fara neman jinjirin wata a ranar Laraba kuma su kai rahoto ga gunduma ko kauye mafi kusa don sanarwa Sarkin Musulmi,” in ji sanarwar.
Ya kuma roki Allah da ya taimaki al’ummar musulmi wajen gudanar da ayyukansu na addini.
Watan Zul-Hijjah shi ne na 12 kuma wata na karshe a kalandar Musulunci inda ake gudanar da aikin Hajji mai tsarki da kuma Idin Kabir – idin layya.
A wani labarin kuma na daban.
Gwamnan Bagudu zai rabawa Manoma 7,9000 kayayyakin aikin gona, Kudin su ya kai naira billiyan biyu
Gwamnatin Jihar Kebbi ta fara rarrarba kayayyakin aikin gona ga , manoma 7,900 ga manoma karkashin shirin nan na KB CARES, a shirin tallafin bankin duniya.
Majiyar jaridar Dimokuradiyya ta ruwaito cewa, Za a rarrarba Kayyakin aikin da kudinsu ya kai Naira biliyan 2 zuwa manoman da ke fadin jihar nan.
Kwamishinan Noma da albarkatun kasa Alhaji Maigari Abdullahi Dakingari ne ya bayyana hakan a lokacin da yake kaddamar da rarraba kayyakin ga manoma a ofishin Hukumar bunkasa Ayyukan gona ta jihar Kebbi dake Kalgo.
Bayanai sun nuna cewa tuni kashin farko suka karbi na su kason.
Kwamishinan yace an rarraba Kayyakin ne ga ƙananan manoman domin tallafa musu da ingantatun iraruwa, magungunan feshi da takin zamani, domin rage musu illar da cutar Korona ta yi a bangaren noma.
Dakingari ya kara da cewa karkashin shirin za’a gina tituna domin samun sauƙin zirga-zirga kayyakin zuwa manya manyan garuruwa daga karkara .
Ana sa bangaren Gwamnan Jihar Kebbi wanda Kwamishinan kasafi da tsare-tsaren tattalin arziki Dakta Abba Sani Kalgo ya wakilta, ya bayyana cewa baya ga Naira miliyan Ashirin da Bankin Duniya ya bayar, sun kara Naira biliyan uku, domin tabbatar da shirin ya kai wurare da dama a cikin jihar nan.