Shugabanin kungiyar kasashe 7 da suka fi karfin tattalin arzikin a duniya sunyi alƙawarin cigaba da baiwa kasar Ukraine tallafi na tsawon lokacin da yakin ta da Rasha zai dauka.
Majiyar jaridar Dimokuradiyya ta ruwaito cewa, Kungiyar ta bayyana hakan ne a rana ta biyu na babban taron su da ke gudana a kasar Jamus.
Haka kuma kungiyar tace dole ne Rasha ta rinka bari ana fitar da abinci daga tashoshin jiragen ruwan Ukraine.
Da yake hallatar taron ta kafar Intanet, Shugaban Ukraine ya yi kira ga kasashen yamma da su baiwa kasar manyan makamai.
A halin da ake ciki yanzu, kasashen G7 na fuskantar kalubale wurin dunkulewa domin tunkarar kasar Rasha dake kara matsa kaimi a Ukraine.
A sanarwar da kungiyar ta fitar a jiya Litinin, tace zata ci gaba da baiwa kasar Ukraine tallafi kuɗi, ayyukkan jinkai, Soji da kuma tallafi Difloma masiya tsawon lokacin da lamarin zai dauka.
Shugabannin kungiyar ta G 7, da suka hada da; Kanada, Faransa ,Jamus. Italiya, Japan , Birtaniya sun hallaci taron da ke gudana a Birnin Bavaria na ƙasar ta Jamus.
Bayanai sun nuna cewa an tattauna muhimman abubuwa da dama , a dai dai lokacin da dakarun Rasha ke ci gaba da kai farmaki a Ukraine, inda mahukunta suka tabbatar da cewa makaman Rasha sun tarwatsa wani rukunin shaguna dake tsakiyar birnin Kremenchuk, wanda ya kashe akalla mutum 10 kamar yadda gwamnan yankin ya bayyanawa kafafaen yada labarai.
A wani labarin kuma na daban.
Ku Fara Duba Jinjirin Watan Sallah A Gobe Laraba—- Sarkin Musulmi Ga Al’umar Musulman Najeriya
Mai Alfarma Sarkin Musulmi kuma Shugaban Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci ta Najeriya (NSCIA), Alhaji Sa’ad Abubakar III, ya umarci al’ummar Musulmi da su duba jinjirin watan Dhul-Hijja tun daga gobe Laraba.
Sarkin ya yi wannan kiran ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Farfesa Sambo Junaidu, shugaban kwamitin ba da shawara kan harkokin addini na Majalisar Sarkin Musulmi ta Sokoto.
“Wannan yana sanar da al’ummar musulmi cewa ranar Laraba 29 ga watan Yuni, daidai da 29 ga Zul-Qidah 1443AH, ita ce ranar da za a fara duba jinjirin watan Dhul-Hijjah 1443AH.”
Sanarwar ta kara da cewa, “Saboda haka an bukaci musulmi da su fara neman jinjirin wata a ranar Laraba kuma su kai rahoto ga gunduma ko kauye mafi kusa don sanarwa Sarkin Musulmi,” in ji sanarwar.
Ya kuma roki Allah da ya taimaki al’ummar musulmi wajen gudanar da ayyukansu na addini.
Watan Zul-Hijjah shi ne na 12 kuma wata na karshe a kalandar Musulunci inda ake gudanar da aikin Hajji mai tsarki da kuma Idin Kabir – idin layya.