Ku Gaggauta Samar da Shirin Kare Ambaliyar Ruwa A Cikin Kwanaki 90 – Buhari ga Minista
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umarci Ministan Albarkatun Ruwa da ya jagoranta tare da haɗa kai da Ma’aikatun Muhalli da Sufuri da kuma Gwamnatocin Jihohin kasar domin samar da wani cikakken shiri na dakile bala’in ambaliyar ruwa a Najeriya.
KARANTA WANNAN LABARIN: Zamfara Ta ɗage Haramci Tarukan Siyasa, ta buɗe Kasuwanni da Makarantu
Wannan umarni zuwa ga ministan na ƙunshe ne a wata takarda mai ɗauke da sa hannun shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Ibrahim Gambari.
Mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu, a wata sanarwa da ya fitar jiya, ya ce Buhari, wanda a kai a kai yake samun bayanai kan halin da ake ciki na ambaliya a kasar, ya nanata kudurinsa na magance kalubalen da bala’in ya janyo a kasar.
A wani labarin kuma: An Hallaka Kwastam ɗaya tare da Jikkata 3 bayan masu Ƙwauri sunyi arangama da Jami’ai a Kwara
Wani jami’i mai suna Saheed Aweda ya rasa ransa sannan wasu uku suka samu raunuka yayin da wasu da ake zargin ‘yan fasa kwauri ne suka bude wuta kan jami’an hukumar hadin gwiwa ta (JBPT) na hukumar kwastam ta Najeriya.
An yi zargin cewa maharan sun yi wa jami’an kwanton bauna ne da ke sintiri a karamar hukumar Baruten ta jihar Kwara.
Jami’an da suka tsira sun samu munanan raunuka a halin yanzu suna karbar magani a wani asibiti da ba a bayyana ba.