Babban sufeton ‘yan sandan kasar nan Usman Baba Alkali, ya shawarci ‘yan sanda a kasar da su guji yin sintiri a gidajen karuwai da gidajen giya domin gujewa hare-haren daga masu tada kayar baya
Alkali ya bayar da wannan shawarar ne a lokacin da yake jawabi ga jami’an rundunar dake Gombe a ziyarar da ya kai shelkwatar rundunar ‘yan sandan jihar.
A cewarsa, yanzu haka jami’an ‘yan sanda sun shiga cikin mawuyacin hali, saboda suna fuskantar barazana daga mayakan IPOB, Boko Haram, ISWAP, ‘yan fashi da makami da masu garkuwa da mutane da dai sauransu.
Ya umarce su da su kasance masu taka tsantsan da lamurorin tsaro ta hanyar gujewa irin wadannan wuraren domin kada su zama masu cikin wadanda farmakin yan ta’adda zai shafa cikin sauki.
Ba Zai Yiwu Ka Tallata Tinubu, Kuma Har Kayi Nasara, Ba Ai Maka Kallon Wa-wa Ba—Dino Melaye
Shugaban ‘yan sandan yayin da ya yi kira ga jami’an sa da su rika gudanar da ayyukansu a kodayaushe ta hanyar bin doka da odan ayyukansu, ya yi gargadin cewa cin zarafin jama’a na jawo daukar tsauraran matakai.
“Cin zarafin farran hula laifi ne, kuma babban laifi ne. Yana da hukunci mai tsanani kama da fashi da makami. Don haka ba za mu iya zama da ‘yan fashi da makami a tsakaninmu ba, ko kuma muna ɗaukaka ‘yan fashi da makami a cikin kakin ’yan sanda ba. Kuna buƙatar kasancewa masu da’a, kuma kuna buƙatar zama ƙwararru,” in ji shi.
IGP wanda ya bayyana cewa a baya-bayan nan an kori wasu jami’an da ake zarginsu da karbar kudi hannun mutane ba bisa ka’ida ba, da kuma rashin sanin makamar aiki, ya bayyana kudurin ‘yan sandan da ke karkashinsa na horar da jami’an ‘yan sanda tare da issasshen horawa, domin bunkasa ayyukansu.
Wannan na zuwa ne yayin da rundunar ‘yan sandan reshen jihar Legas, ta sallami wani jami’inta, kofral Opeyemi Kadiri, saboda binciken lambar wayar wani matafiyi.
An sallami jami’in ne bayan da na’urar daukar bidiyo ta nuna shi yana binciken wayar mutumin a gefen hanya wanda kuma hakan ya sabawa umurnin da sufeto janar na kasar Usman Alkali Baba ya bayar.
A cikin bidiyon, an ji yo matafiyin na kokawa da nuna rashin amincewa kan bukatar da jami’in dan sandan ya yi na binciken wayarsa, inda ya ce sufeto ‘yan sandan kasar ya hana yin hakan, amma jami’in yaki saurara masa.
Kadiri dai na aiki ne da rundunar ‘yan sandan jihar Legas a shiyyar Dolphin