Tsohon dan majalisar tarayya, Sanata Dino Melaye, ya bayyana cewa ba zai yuwu a tallata jam’iyyar APC, da dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar, Bola Ahmed Tinubu ba tare da an kalli mutum a matsyain wawa.
Dino, wanda ya bayyana hakan a wani shirin gidan talabijin na Channels a ranar Juma’a, ya ce gazawar gwamnatin APC ya sanya ‘yan takarar jam’iyyar su, zai yi matukar wuya su samu karbuwa a fadin kasar nan.
A cewar tsohon dan takarar gwamna a jihar Kogi, Tinubu da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour, Peter Obi ba su da wata alama da jza su iya gwamzawa da dan takarar shugaban kasa na Jam’iyar PDP, Atiku Abubakar.
Dino wanda kwanan nan aka nada a matsayin mai magana da yawun kwamitin yakin neman zaben Atiku, ya kuma caccaki Ministan Kwadago da samar da Ayyukan yi Festus Keyamo kan kalaman da ya yi kan Tinubu a kwanakin baya.
Ku Bayyana Ni A Matsayin Dan Takarar PDP A Jihar—-Abacha Ya Gayawa INEC, PDP
Ya ce, “Wannan gwamnati ta tallata Atiku ne ta hanyar gazawarta. A yau, dan takarar da ya fi kowa wahala a tallata shi, shi ne dan takarar jam’iyyar APC walau a matakin majalisar wakilai ko Sanata ko Gwamna.
“Shi ya sa ba za ka iya kare, tallata ko yi wa Bola Ahmed Tinubu yakin neman zabe ba tare da an kalleka a matsayin wawa ba.” Inji shi.
“Wannan shi ne abin da ya faru da ɗan’uwana kuma abokina, Festus Keyamo, ya fara magana ba tare da wata hujja gamsasshiya ba. Ya fara fadin abubuwan da ba su da ma’ana.”