Daga Adamu Albarkawa Kaduna
Wani jigon jami’iyar APC a shiyyar Arewa maso yamma Alh. Babangida fate, ya yi suka da kakkausar murya ga wasu daga cikin gwamnonin Arewacin kasar, bisa halin ko-in-kular da suke nunawa game da harkokin da suka shafi Arewacin kasar nan.
A ganawar shi da Jaridar Dimokaradiyya, a kaduna, Alh. Babangida fate, ya ce abun bakin Ciki ne game da yadda wasu gwamnanonin arewa ke wa sha’anin tsaro rikon sakainar kashi a jahohinsu, Wanda hakan a cewar sa bai dace ba, domin kuwa talakawan da suka zabe su ne ke Dandana kudarsu a rashin tsaron da ke aukuwa a yankin Arewan.
Ya kara da cewa, wani abun ban haushi ma shi ne yadda idan an zo taron gwamnonin Arewa kalilan daga cikin su ne ke halartar taron, amma kuma Idan aka ce taro ne zasu yi da shugaban kasa a lokacin ne kowane daga cikinsu kan kwashe kwanaki a Abuja.
Da yake sokaci game da taron da aka yi na Gwamnonin Arewa a nan kaduna, Alh. Babangida fate, yace daya bisa uku na gwamnonin basu halarci taron ba, ya ce wannan abun damuwane matuka.
Daga nan jigo a jamiyar APC Alh. Babangida fate, ya yi kira ga al’ummar arewa da su sanya idanu sosai da kuma bibiyar ayyukan kowane Dan siyasa domin sanin Wanda zasu marawa baya a duk lokacin da aka zo zabe, inji shi.