Gwamna Bello Mattawale na jihar Zamfara a jiya ya haramta hawan babura daga karfe 8 na dare zuwa 6 na safe a garin Gusau.
Ya umurci jami’an tsaro da su harbe duk wanda aka samu ya saba wa sabuwar dokar.
Batun Ficewar Sanata Shekarau Daga NNPP Zuwa PDP Shifcin Gizo ne
A cewar gwamnan, sun dauki matakin ne biyo bayan rahotannin yadda ‘yan bindiga da sauran masu laifi ke amfani da babura wajen aikata muggan laifuka a cikin babban birnin jihar da kuma makotan birnin.
Ya ce, “Idan aka yi la’akari da farmakin da ‘yan bindiga suka kai a wasu yankuna da ke wajen Gusau, babban birnin jihar, ya sanya aka hana hawan babura daga karfe 8 na dare zuwa 6 na safe a dukkan yankunan da wajen garin Gusau.
“Gwamnatin jihar ba za ta yi wasa da duk wanda aka samu yana kawo cikas ga zaman lafiya da tsaron jama’a ba”.
Gwamnan ya jaddada cewa, tsaron rayuka da dukiyoyin ‘yan kasa shi ne babban aikin kowace gwamnati.
“Gwamnatina tana yin duk mai yiwuwa ga kula da yan Zamfara, bisa ga dokokin kasa don tabbatar da sauke wannan nauyi.” inji Matawalle.