Gwamnatin jihar Zamfara ta rattaba hannu a kan hukuncin kisa ga duk wanda aka samu da laifin aikata fashi da makami, satar shanu, kungiyar asiri, ko kuma mai taimaka yan Garkuwa da ‘yan fashi da bayanan sirri.
Gwamna Bello Matawalle ne ya bayyana hakan yayin jawabi kai tsaye ga al’ummar jihar, a safiyar Talatar nan.
Matawalle ya ce, “A ranar 28 ga watan Yuni na wannan shekara, na sanya hannu kan kudirin dokar haramtawa da hukunta masu fashi da makami, satar shanu, garkuwa da mutane da sauran wasu muggan laifuka 2022.
“Dokar ta ba da ka’idar doka don hukunta masu aikata laifin fashi da makami.
Dangane da sabuwar dokar, duk wanda aka samu da laifin aikata fashi, garkuwa da mutane, satar shanu, kungiyar asiri, ko kuma yin aiki a matsayin mai ba da bayanan sirri ga barayi shima zai fuskanci hukuncin kisa.
“Hakazalika, duk wanda aka samu da laifin goyon baya kan laifukan da aka ambata a sama, ta kowace fuska shima zai fuskanci hukuncin daurin rai da rai, ko zaman gidan yari na shekaru 20, ko kuma na shekaru goma, ba tare da zabin tara ba.”
Gwamnan ya bayyana cewa matakan na daga cikin kokarin gwamnatin sa na ganin an shawo kan matsalar ‘yan fashin da suka addabi jihar da kuma jihohin arewa maso yammacin kasar sama da shekaru goma.
Ya ci gaba da cewa tun daga lokacin da gwamnatinsa ta karbi mulki ya fara bullo da dabarun dakile matsalar ‘yan fashi a fadin jihar.
“Abin farin ciki, sabbin matakan sun fara samar da sakamakon da aka yi niyya duk kuwa da hare-haren da ‘yan bindiga ke kaiwa nan da can,” in ji Matawalle.
Gwamnan ya bayyana ayyukan masu bayar da bayanan Sirri, da cewa wani babban kalubalen rashin tsaro ne a jihar, inda ya bayyana kwarin gwiwar cewa nan ba da jimawa ba lamarin zai zo karshe.