- Tsohon gwamnan jihar Akwa Ibom, Godswill Akpabio, ya yi kira ga ‘yan Najeriya da kada su tantance shi a matsayin ministan harkokin raya yankin Neja Delta.
- “Ba zan so a hukunta ni da nadin minista a Neja-Delta ba, wanda kowa ya san wuri ne mai matsala.”
- Akpabio yace gwara ayi masa hukunci a matsayinsa na lauya, kwamishina na shekara shida da kuma gwamna na shekara takwas.
Tsohon gwamnan jihar Akwa Ibom, Godswill Akpabio, ya yi kira ga ‘yan Najeriya da ‘yan majalisar dattawa ta 10 mai zuwa da kada su tantance shi ta hanyar amfani da takaitaccen lokacin da ya rike a matsayin ministan harkokin raya yankin Neja Delta.
Akpabio ya ce ya fi son a yi masa shari’a a matsayinsa na lauya mai shekaru 36, kwamishina na shekara shida da gwamna na shekara takwas.
KARANTA WANNAN LABARIN: Tafaru Ta Kare: Likitocin Masu Neman Kwarewa Sun Janye Yajin Aikin Gargadi
Ya bayyana haka ne a wata hira da manema labarai a Abuja a daren ranar Asabar.
Jaridar PUNCH ta rawaito cewa, Akpabio, wanda shi ne zababben Sanata mai wakiltar Akwa Ibom ta Arewa maso Yamma, daya daga cikin masu neman kujerar shugabancin majalisar dattawa ta 10, wanda aka shirya kaddamar da ita a ranar 6 ga watan Yuni.
A shekarar 2015 ne aka fara zabar shi a majalisar dattawan Najeriya inda ya zama shugaban marasa rinjaye a jam’iyyar PDP amma daga baya ya koma jam’iyyar APC mai mulki.
Akpabio ya yi murabus daga mukaminsa na Ministan Harkokin raya yankin Neja-Delta domin ya tsaya takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC a zaben 2023 amma daga baya ya bar wa zababben shugaban kasa, Asiwaju Bola Tinubu takara.
Duk da cewa zababben dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC ne ya zabo shi, tsohon gwamnan jihar Zamfara, Abdulaziz Yari, da kuma dan majalisar dattawa, Orji Uzor Kalu, sun sha alwashin ba za su sauka daga takarar shugabancin majalisar dattawa ba.
“Na san cewa ban canza ba ta kowace hanya. Ni mutum ne da Allah Ya ba shi sa’ar da ba a saba gani ba a duk inda na shiga. Ba zan so a hukunta da nadin minista a Neja-Delta ba, wanda kowa ya san wuri ne mai matsala.
“Amma ina so a hukunta ni a matsayina na lauya mai shekaru 36, kwamishina na shekara shida da kuma gwamna na shekara takwas,” in ji Akpabio.
Idan dai za a iya tunawa,JARIDAR DIMOKURADIYYA ta rawaito cewa a watan Yulin shekarar 2020, a lokacin da Akpabio ke rike da mukamin ministan harkokin raya yankin Neja-Delta, ya bayyana gaban kwamitin majalisar wakilai kan yankin Neja Delta, a wani zaman binciken kwakwaf na Naira biliyan N81.5bn da ma’aikatar ta kashe tsakanin watan Janairu zuwa Yulin shekarar 2020.
Akan kudirinsa na tsayawa takarar shugabancin majalisar dattawa, Akpabio ya yi alkawarin cewa idan aka zabe shi, zai dore da tsarin kasafin kudin watan Janairu zuwa Disamba da majalisar wakilai ta 9 ta fara.
A cewarsa gabatar da tsarin kasafin kudin watan Janairu zuwa Disamba na daya daga cikin manyan nasarorin da majalisar ta samu.
Ya kuma bayyana dangantakarsa da wasu abokan aikinsa masu adawa da burinsa.
“A batun ko wani ya goyi bayan ko a’a, ba batun bane. Maganar ita ce dole ne mu ci gaba da shiga. Allah ya hada mu da shekaru hudu masu zuwa.
“Dole ne mu ci gaba da yin magana da mutane domin duk wani ra’ayi da suke da shi wanda da gaske ba daidai ba game da ni za a yi watsi da shi gaba daya,” in ji shi.
A wani labarin kuma, Kaso 70% Na Kayan Da Aka Sarrafa Najeriya Ƙasashen Waje Basa Karba – NAFDAC
Darakta-Janar ta hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa NAFDAC, Farfesa Mojisola Adeyeye ta ce sama da kashi 70 cikin 100 na kayan abinci da ake fitarwa daga Najeriya ana ƙin karbar su a kasashen waje.
Farfesa Adeyeye ta bayyana haka ne a wajen kaddamar da sabon ofishin NAFDAC na filin jirgin sama na Murtala Muhammed dake a jihar Legas.