Ku Rika Fitar Da Zakka Don Rage Radadin Talauci A Najeriya – Kungiyar Musulmi Ga Attajirai
Kungiyar Musulmi ta Najeriya (MAN) ta yi kira ga al’ummar Musulmi masu hannu da shuni a fadin kasar nan da su fitar da zakka a lokacin da ya kamata.
Kungiyar ta bayyana cewa hakan ya zama dole domin rage radadin talauci a kasar.
KARANTA WANNAN LABARIN:Gwamnatin Kano zata baiwa nakasassu tallafin karatu zuwa kasashen waje
Bayar da zakka ita ce rukunnan addinin Musulunci na uku.
Sai dai ta umurci attajirai maza da mata na addinin Musulunci da su fitar da zakka, domin dinke barakar da ke tsakanin masu hannu da shuni a cikin al’umma.
Shugaban kungiyar, reshen Ibadan, Rahman Olawale AbdulGaniy ne ya bayyana hakan bayan raba kudaden zakka (sadaka) ga mutane 35 da suka amfana daga jihar Legas da Oyo.
AbdulGaniy wanda ya zanta da wakilinmu a ranar Alhamis bayan kammala rabon, ya bayyana cewa an baiwa wadanda suka ci gajiyar tallafin kayan aikin karfafawa a lokacin rabon zakka.
AbdulGaniy ya kuma yi kira da a rika ba da gudunmuwar a kai a kai da kada a yi kasa a gwiwa wajen yin hakan, inda ya kara da cewa talauci zai ragu idan masu arziki a cikin al’umma za su fitar da zakka.
Ya ce, “Ina so in yi kira ga masu hannu da shuni da su rika fitar da zakka. Za mu raba shi ga matalauta. Hakan zai taimaka mana wajen rage talauci. Gwamnati ba za ta iya yin komai ba.
A wani labarin kuma:Shugabannin Sojoji sun isa Majalisa don tantace su
A ranar Alhamis ne sabbin shugabannin sojoji da aka nada suka isa majalisar dokokin kasar domin tabbatar da nadin nasu kamar yadda dokar majalisar ta tanada.
Manyan hafsoshin tsaron da su hudu ne shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya nada su bayan mika sunayensu ga majalisar dattawa domin tantance su.