- Oluwarotimi Akeredolu, gwamnan jihar Ondo, ya bukaci sabbin ‘yan majalisa da su sanya bukatun al’umma agaba wajen gudanar da ayyukansu.
- Gwamnan ya bukaci ‘yan majalisar su dauki nauyin da ke kansu a matsayin hidima ga mutanen da suka zabe su.
- Kada ku kasance masu nuna bangaranci da gudanar da ayyukan ku ba tare da wani tsoro, son rai, ko tsangwama ba.
Oluwarotimi Akeredolu, gwamnan jihar Ondo, ya bukaci sabbin ‘yan majalisar jihar da aka kaddamar da su baiwa bukatun al’umma fifiko wajen gudanar da ayyukansu,Daily Post ta rawaito.
A wata sanarwa da babban sakataren yada labaran sa, Richard Olatunde ya fitar, gwamnan ya jaddada cewa ya kamata ‘yan majalisar su dauki nauyin da ke kansu a matsayin hidima ga mutanen da suka zabe su a matsayin wakilansu.
KARANTA WANNAN: Gwamnati Mai Ci Ta Wucin Gadi Ce, Zan Karbo Kujerata A Kotu – Atiku Ga Tinubu
Akeredolu wanda tun da farko ya taya sabon shugaban majalisar murna da kansa, ya kuma bukaci ‘yan majalisar da kada su kasance masu nuna bangaranci da gudanar da ayyukansu ba tare da wani tsoro, son rai, ko tsangwama ba.
Ya kuma yabawa ’yan majalisar kan zaben shugabanninsu ba tare da wani rikici ko rashin fahimta ba.
Gwamnan ya jaddada cewa doka tana taka muhimmiyar rawa wajen tsarawa, haɓakawa, da daidaita al’umma, da kuma kiyaye ƴan ƙasa.
“Dokoki muhimmin aiki ne kuma daya daga cikin muhimman kayan aikin gwamnati wajen tsarawa, bunkasawa, da daidaita al’umma da kuma kare ‘yan kasa.
“Ina taya sabbin ‘yan majalisar mu da aka rantsar murna. Mutanen ku sun ba da amana da amincewa a gare ku. Dole ne ku yi ƙoƙari ku tabbatar da wa’adin da jama’a suka zuba muku ta hanyar wakilci mai inganci,” in ji shi.
A wani labarin kuma, Wasu Sabbin Gwamnoni Sun Koka Game Da Tarin Basussukan da Suka Tarar
Tuni dai wasu daga cikin sabbin gwamnonin jihohin da aka rantsar da su ke kan hanyar yaki tare da magabatan su kasa da mako guda da hawansu ragamar mulki,The Nation ta rawaito.
A jiya ne Abba Yusuf na jihar Kano ya kaddamar da ruguza gine-gine a filin Sukuwa na Kano da kuma wasu wuraren gwamnati a cikin babban birnin jihar wanda tsohon Gwamna Abdullahi Ganduje ya amince da shi.