- Rikici tsakanin sabbin gwamnoni da magabatansu kan yadda suka bar musu dumbin bashi.
- Gwamnatin Kano ta fara rusa gidajen da Ganduje ya amince da shi
- Ku Maido Da Dukkan Motocin Hukuma Cikin Kwanaki Biyar Gwamnan Zamfara Ya Gargadi Matawalle.
Tuni dai wasu daga cikin sabbin gwamnonin jihohin da aka rantsar da su ke kan hanyar yaki tare da magabatan su kasa da mako guda da hawansu ragamar mulki,The Nation ta rawaito.
A jiya ne Abba Yusuf na jihar Kano ya kaddamar da ruguza gine-gine a filin Sukuwa na Kano da kuma wasu wuraren gwamnati a cikin babban birnin jihar wanda tsohon Gwamna Abdullahi Ganduje ya amince da shi.
KARANTA WANNAN: Kungiyar Kwadago Ta Nemi Hadin Kan ASUU Domin Tsunduma Yajin Aiki
Yusuf ya caccaki yadda aka gudanar da gine-ginen a matsayin haramtattu.
JARIDAR DIMOKURADIYYA ta rawaito cewa gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal ya baiwa magabacinsa Bello Matawalle da mataimakinsa wa’adin kwanaki biyar da su mayar da dukkan motocin gwamnati da ke hannunsu.
Lawal ya zargi Matawalle da tafiya da dukkan motocin gwamnati da (Matawalle) ya ce ya siya a kan jimillar kudi N2,794,337,500.
Sabon Gwamnan Jihar Akwa Ibom, Umo Eno, ya samu bashin Naira Biliyan 264 daya gada ina yake neman hanyar magance shi yayin da Peter Mbah na Jihar Enugu, Uba Sani na Jihar Kaduna da Caleb Mutfwang na Jihar Filato ke zufa saboda kalubalen tsaro da suka gada daga magabata. .
Yusuf, wanda ya sha alwashin bayan ya karbi ragamar shugabancin Kano a ranar Litinin da ta gabata don kaddamar da bincike kan bashin zabar kudi har naira biliyan N241bn da Ganduje ya gadar masa.
Abba Gida-Gida a jiya ya jagoranci ruguje gine-gine da dama a cikin babban birnin Kano, bisa zargin cewa an yi gine-gine a filayen gwamanati.
Da yake bayyana manufar sa a shafinsa na Twitter @Kyusufabba, gwamnan ya ce: “Da sanyin safiyar ranar Asabar, mun shaida yadda aka fara aiwatar da matakin farko a yunkurinmu na dawo da hayyacin tsarin raya birane na jihar Kano.
“Tare da rusa wannan haramtaccen ginin da aka yi a filin wasa na Race Course, mun tashi tsaye don kwato duk wani fili da aka boye a wuraren gwamnati wandanda suka gano an yi amfani da su wajen kafa haramtattun gine-gine da masu zaman kansu ko kungiyoyi suka yi.
“Na kuma ba da umarnin rusa duk wasu gine-ginen da aka gina ba bisa ka’ida ba a makarantu, masallatai, wuraren wasan yara, makabarta, kasuwanni da asibitoci, domin tabbatar da bin ka’idar tsara birane, kawatawa da kuma kare lafiyar jama’a.
Ku Maido Da Dukkan Motocin Hukuma Cikin Kwanaki Biyar, Gwamnan Zamfara Ya Gargadi Matawalle
Lawal, a wata sanarwa da ya fitar ta hannun babban mai taimaka masa na musamman kan harkokin yada labarai, Sulaiman Bala Idris, ya ce Matawalle ya yi ikirarin kashe zunzurutun kudi har Naira biliyan 2,794,337,500 don siyan motocin gwamnati amma babu ko daya daga cikin motocin a gidan gwamnati.
A cewarsa: “Tsohon gwamnan ya bayar da kwangilar siyan motocin da za a raba wa manyan ma’aikatu da hukumomi (MDAs) a kan kudi naira biliyan daya da dari daya da arba’in da tara da miliyan dari takwas. (N1,149,800,000.00).
Yadda Kudaden Gwamnatin Jihar Akwa Ibom Suka Kasance Ba Su Yi Wa Sabon Gwamna Fasto Umo Eno Dadi Ba.
Shugaban gamayyar kungiyoyin fararen hula a jihar Akwa Ibom, Mr. Harry Udoh, ya yi zargin cewa gwamnatin Udom Emmanuel ta bar basussukan da suka kai tsabar kudi Naira biliyan 264 a baya.
An tattaro cewa shugabannin jam’iyyar PDP a jihar su ma suna kara matsa lamba kan Udo kan wanda ya dace ya kasance a cikin majalisarsa.
Samar da ababen more rayuwa, samar da ruwa, samar da ayyukan yi na kan gaba a kalubalen Mbah
Gwamna Otti Na Abia Ya Fusata Kan ‘Wawashe Dukiyar Jihar‘
Gwamnan jihar Abia, Alex Otti, ya ce ya gaji baitul malin da aka yi wa barna har ta kai ga cewa muna da Naira biliyan 50 da ba a biya albashi ba, kyauta da kuma fansho.
Wato baya ga cikar bashin gida da waje da suka lakume Naira biliyan 200 da sauran basussukan ‘yan kwangila.
Sanata Uba Sani Yana Fuskantar Kalubalen Tsaro
Da kyar Gwamnan Jihar Kaduna Uba Sani ya gusar da gajiyar da aka yi na rantsar da shi a ranar Litinin din da ta gabata, inda aka samu labarin sace Shugaban Matan Jam’iyyar APC na Birnin-Gwari, Hajiya Lami Awarware, da mataimakiyar ta Hajiya Haulatu Aliyu da wasu da dama yayin da suke dawowa zuwa Birnin-Gwari daga Kaduna bayan halartar bikin rantsar da shi.
Rashin tsaro dai na daya daga cikin kalubalen da ya gada a jihar da ‘yan bindiga ke kashewa tare da raunata mutanen da ba su ji ba ba su gani ba.
Rikicin da ake fama da shi ya durkusar da tattalin arzikin al’ummar karkara wadanda kusan manoma ne a kananan hukumomin Birnin Gwari da Chikun da Igabi da Giwa tare da talauta jama’a da kuma jefa da dama cikin kabari.
Nan take ya kira taron majalisar tsaro a ranar Larabar da ta gabata, inda ya yi alkawarin tallafa wa hukumomin tsaro na tarayya a jihar, don ba su damar kawar da duk wani nau’i na laifuka a jihar.
Gwamnan a wurin taron ya nuna damuwarsa tare da jaddada cewa tsaro wani babban ginshiki ne na tsare-tsare guda 7 na gwamnatinsa, ya kuma bukaci shugabannin hukumomin tsaro da su saukaka ko kuma shirya taron tsaro na bai-daya da nufin inganta cudanya da al’umma da samar da wayar da kan jama’a game da tsaro.
Taron ya samu bayanai kan kalubalen tsaro da ya taso daga ayyukan ‘yan fashi, garkuwa da mutane, rigingimun jama’a, sace-sacen waya, barazanar karancin man fetur, da kuma fadan ‘yan kungiyar (sara suka).
Shima Dai Gwamna Mutfwang na Jihar Plateau Hakan Take
Kamar Sanata Uba Sani dake makwabciyar jihar Kaduna, gwamnan jihar Filato Mutfwang yana da babban kalubalen tsaro da zai iya magancewa.
Baya ga daruruwan mutanen da ‘yan bindiga suka kashe, a halin yanzu akalla ‘yan jihar 20,000 ne ke zaune a sansanonin ‘yan gudun hijira na jihar.
An yi jana’izar kusan mutane 200 a sabon harin da aka kai a jihar kwanan nan.
Ya kuma gaji bashin Naira biliyan 200 daga tsohon gwama Lalong.
Mutfwang ya ce a fili ya fahimci “girman aikin da ke gabana kuma ba ni da tunanin cewa zai zama tafiya mai sauki.”
Ya ce bai kamata jama’a su yi tsammanin za a yi gaggawar gyara ba.
A wani labarin kuma, Gawuna Ya Ziyarci Ganduje A Gidansa Na Abuja
Tsohon Gwamnan jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya karbi bakunci wasu daga cikin tawagar tsohuwar gwamnatinsa.
Tawagar bisa jagoranci Dr Nasiru Yusuf Gawuna, sun ziyarci Gwamnan me, wanda yanzu haka ke gidansa na Abuja.