Ku taimaka mana wajen yaƙar satar mai – NDDC ta roki sarakunan gargajiyan Ribas
Hukumar Raya yankin Neja-Delta, NDDC, ta bukaci hadin kai da taimakon sarakunan gargajiya wajen yaki da satar mai a jihar Ribas.
Babban daraktan kudi na NDDC, Boma Iyaye ne ya yi wannan kiran yayin taron tattaunawa da hukumar da ‘yan majalisar sarakunan gargajiya ta jihar Ribas, ranar Talata a Fatakwal.
KARANTA WANNAN LABARIN:Ƴan sanda sun fito da wani gargaɗi kan wani take da ake amfani da shi
Wakilin NDDC na jihar Ribas, Tony Okocha da Iyaye sun ziyarci majalisar sarakunan gargajiya, domin yin cudanya da ingantattun hanyoyin samun ci gaba a jihar.
Da yake jawabi ga majalisar gargajiya, Iyaye ya bayyana cewa shugabannin al’ummomi daban-daban na da rawar da suke takawa wajen taimakawa gwamnati da hukumomin tsaro wajen tabbatar da dukiyar jihar da kuma dakile satar mai.
A cewar Iyaye, idan aka yaki da satar mai a yankin, Najeriya za ta kara samar da kudaden shiga, sannan ta kara kudaden da ake warewa yankin na Neja Delta.
Iyaye ya ce, “Zan yi kira ga manyanmu da masu girmanmu, kuna da rawar da za ku taka.
“Aikin shi ne, ta yaya kuke taimaka wa gwamnati wajen kare kadarorinmu na man fetur? Ta yaya kuke taimakawa hukumomin tsaro don kare jihar daga satar mai? Domin kun san wasu daga cikin waɗannan mutanen da suke yin wannan aikin.
A wani labarin kuma:Gwamnatin Najeriya na neman haɗin gwiwa da kungiyoyin kwadago don kyautatawa Ma’aikata
Gwamnatin tarayya ta bukaci hadin kan kungiyar kwadago ta Najeriya NLC, wajen inganta jin dadin ma’aikata da kuma samar da ci gaban kasa.
Karamar ministar kwadago da samar da ayyukan yi, Mrs Nkeiruka Onyejeocha, wacce ta bayyana hakan a wata ziyara da ta kai wa shugabannin kungiyar ta NLC ranar Alhamis a Abuja, ta kara da cewa hadin gwiwar zai baiwa bangarorin biyu damar magance duk wani abu da ya shafi ma’aikata a kasar.