Gwamnatin Najeriya na neman haɗin gwiwa da kungiyoyin kwadago don kyautatawa Ma’aikata
Gwamnatin tarayya ta bukaci hadin kan kungiyar kwadago ta Najeriya NLC, wajen inganta jin dadin ma’aikata da kuma samar da ci gaban kasa.
Karamar ministar kwadago da samar da ayyukan yi, Mrs Nkeiruka Onyejeocha, wacce ta bayyana hakan a wata ziyara da ta kai wa shugabannin kungiyar ta NLC ranar Alhamis a Abuja, ta kara da cewa hadin gwiwar zai baiwa bangarorin biyu damar magance duk wani abu da ya shafi ma’aikata a kasar.
KARANTA WANNAN LABARIN:Tsohon Shugaban Ƙasa Buhari Ya Amshi Baƙuncin Tsaffin Jami’an sa
Ta bayyana cewa ziyarar na daga cikin dabarun da Ma’aikatar ta tsara don zaburar da masu ruwa da tsaki don yin daidai da ajandar gwamnati a bangaren kwadago.
A cewarta, idan ba tare da hadin kan kungiyoyin kwadago ba, zai yi wahala gwamnati ta inganta ma’aikatan Najeriya da dama.
Ministan ya kuma jaddada cewa gwamnati na sha’awar jin dadin ma’aikatan Najeriya, ciki har da lafiyarsu da muhallin da suke aiki.
“Muna kuma sha’awar albashin da suke samu. Za mu yi hadin gwiwa da ku don tabbatar da cewa ma’aikatan Najeriya sun gamsu sun samu jindaɗi.
“Na tabbata za ku ba gwamnati hadin kai don ganin tattalin arzikinmu ya inganta; a duk lokacin da kuka shiga yajin aiki, tattalin arzikin Najeriya ya ragu, kuma muna tafka asara mai yawa,” inji ta
A wani labarin kuma:Ƴan sanda sun fito da wani gargaɗi kan wani take da ake amfani da shi
Rundunar ‘yan sandan Najeriya, NPF, ta gargadi matasan Najeriya da cewa salon da ake yi na ‘no gree for anybody’ na iya haifar da rikici.
Tun daga farkon sabuwar shekara taken ya mamaye shafukan sada zumunta, wanda galibi matasa ne ke amfani da shi.