Gwamnan Kogi Yahaya Bello a ranar Juma’a ya bayar da umarnin a dawo da ‘yan majalisar dokokin jihar Kogi da aka dakatar.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Majalisar dai ta dakatar da mataimakin shugaban majalisar Ahmed Ahmed, shugaban masu rinjaye Abdullahi Bello da mataimakinsa Moses Ododo bisa laifin rashin da’a.
KARANTA WANNAN LABARIN: Hotuna: Shugaban Majalisar Jiha da Amaryarsa Sun Halarci Liyafar Aurensu a Keke Napep
Amma Gwamna Bello, yayin da yake magana jim kadan bayan amincewa da kudurin kasafin kudin 2023, ya ce ya yafewa duk wanda ya yi masa laifi.
Ya kuma bukaci majalisar dokokin jihar da ta kira ‘yan majalisar da aka dakatar saboda ya jajirce wajen hada kan jama’a domin samun ci gaba a jihar Kogi.
A wani labarin kuma, Wani Magidanci Ya Lakada Wa Diyarsa Duka Har Lahira Saboda Ta Kira Saurayinta Da Layin SIM Dinsa
Rundunar ‘yan sandan jihar Akwa Ibom ta kama wani Akaninyene Okokon bisa zarginsa da lakadawa ‘yarsa ‘yar shekara 16, Abasiono Akaninyene Sunday duka tsiya inda ya kashe ta har lahira.
Kwamishinan ‘yan sanda, Mista Olatoye Durosinmi, ya ce jami’an hedikwatar shiyya ta Ikot Ebo sun kama wanda ake zargin ne biyo bayan samun sahihan bayanai.
Durosinmi ya yi magana ne a ranar Juma’a yayin da yake gabatar da wanda ake zargin tare da wasu mutane 195 da rundunar ta kama bisa laifuka daban-daban da suka hada da garkuwa da mutane, sata, kungiyoyin asiri da fasa bututun mai a hedikwatar ‘yan sanda da ke Ikot Akpanabia, Uyo.