Matar shugaban kasa Muhammadu Buhari ta soki makudan dalolin da aka kashe don siyo gidan sauro a shirin nan mai taken “social Investment Programme”.
Aisha Buhari, ta yi wannan suka ne a yayin taron tattaunawar ta da mata a ranar Asabar a fadar shugaban kasa Buhari.
Inda ta ce “Dala Miliyan $16 da aka barnatar don siyo gidan sauro, zai iya tsaftace Najeriya daga duk wani datti da kazanta.