Tsohon Shugaban kasa Cif Olu Shegun Obasanjo, a jiya ya zargi cewa matsalolin da ake fuskanta a kasar nan kirkirarru ne, inda yace kuma wannan matsaloli ba na kasar nan bane ainihi.
Tsohon shugaban yana wannan magana ne lokacin da yake kaddamar da wani aikin wata makarantar fasahar noma a Ibadan, wacce ta ke daya daga cikin wuraren da ya bude na bincike kan harkar noma na a Afrika.
An fara aikin Ginin tun 2017,inda lokacin ma anyi bikin fara aikin Wanda a wancan lokacin tsohon Shugaban mulkin Soja Yakubu Gowon,Cif Obasanjo,da Shugaban bankin manoma na afrika Dakta Akin Adesina kuma bude shi yayi dai dai da cikar ita (IITA) cika shekaru 50 da kafuwa.
Ginin Wanda bankin manoma ya samar a Najeriya mai taken transformation agenda support program.(ATASP)ya kunci ofisoshi 22da sashen bincike gida 8 da dakin taro.
Da ke kilo mita 10.5km kan hanya da fadin 1000 eka na gun (IITA)Wanda Gwamnatin jahar Oyo ta Gina da kuma Taimakon kungiyar.
Obasanjo ya kara da Cewa kasar nan tana bukatar bullo da wasu dabaru tin a baya yace amma duba abubuwan dake faruwa yanzu yace rashin tsari ne.
A karshe ya yabawa gwamna kan namijin kokarin da yayi na aiwatar da wannan aiki.