Gwamnatin jihar Jigawa ta amince da biyan jimillar Naira biliyan 9.4 a matsayin kudin fansho ga Tsoffin ma’aikatan gwamnati 2,146 da suka yi ritaya a sassa uku na ma’aikatan jihar daga watan Janairu zuwa Disamba na wannan shekara.
Hakan na kunshe ne a taron manema labarai na karshen shekara da Sakataren zartarwa na hukumar fansho na jiha da na kananan hukumomi, Kamilu Aliyu Musa ya yi a Dutse.
Ya kuma ce hukumar ta biya Naira miliyan 488.9 a matsayin kudin albashin watan Disamba ga ma’aikatan gwamnati 209 a jihar.
Musa ya kuma yi kira ga wadanda suka ci gajiyar tallafin da su guji baiwa kowa cin hanci da rashawa a yayin da ake gudanar da raba kudaden, inda ya bukace su da su kai rahoton duk wani ma’aikacin sa da ya nemi cin hancin.
Don haka ya yabawa Gwamna Badaru Abubukar bisa goyon bayan da yake baiwa hukumar tare da gaggauta sakarwa ‘yan fansho hakkokinsu.