Kungiyoyin farar hula da dama sun yi kira ga majalisar dokokin kasar da ta yi wa dokar zabe ta 2022 kwaskwarima ta hanyar sanya adadin da jam’iyyun siyasa za su iya sayar da fom ga masu neman mukaman gwamnati.
Hakan dai na zuwa ne a dai dai lokacin da ‘yan majalisar dokokin kasar suka ce suna duba yiwuwar yin gyaran fuska.
‘Yan majalisar, musamman ’yan majalisar wakilai, sun ce duk da ya kamata a bar jam’iyyu su daidaita kansu, amma kwanan baya Naira miliyan 100 da jam’iyyar APC ta kakaba wa masu neman takarar shugaban kasa na ci gaba da sanya damuwa a zukatan yan kasa.
Da yake zantawa da wakilinmu, Babban Darakta mai fafutukar kare hakkin jama’a da tattalin arziki da kuma tabbatar da daidaiton al’amura, Adetokunbo Mumuni, ya bayyana cewa kamata ya yi a kayyade farashin fom din jam’iyya kafin kashe kudaden yakin neman zabe da kuma bayar da gudunmawa.
Har ila yau, jagoran wata kungiya mai suna ” Concerned Nigerians,” Deji Adeyanyu, ya ce, “Na yarda da cewa ya kamata mu gyara dokar zabe don nuna cewa kada jam’iyyun siyasa su karbi fiye da wani adadin kudi.”
A cewarsa, naira miliyan 100 na fom din APC na zaben shugaban kasa ya wuce gona da iri.