By Abbas Yakubu Yaura
Gamayyar Kungiyoyin Arewa, CNG ta nuna matukar alhinin ta bisa rasuwar dattijon Kano kuma dan takarar shugaban kasa a wani lokaci, Alhaji Bashir Othman Tofa, inda ta bayyana shi da babban jigo kuma mai ba da shawara.
A cikin sakon ta’aziyyar da mai magana da yawunsa kungiyar ta CNG Abdul-Azeez Suleiman ya fitar, ta ce tana matukar godiya ga marigayi Bashir Tofa wanda ya jagoranci, sadaukarwa, kishin kasa, da jajircewarsa wajen kare muradun al’ummar Arewacin Najeriya, da ‘yan Nijeriya a matsayinsa na mai mulki.
“Muna jimamin rasuwar wannan mutumi mai girma wanda muka samu kwarin gwiwa a rayuwarsa da ayyukansa kuma dole ne mu yi ƙoƙari, a duk abin da muke yi, mu rayu bisa ka’idoji na sirri da na zamantakewa da ya rayu kuma ya kafa wa kansa,” in ji shi.
Marigayi Tofa, Suleiman ya ce, ya kasance mai kishin imani da alakar da ke tsakanin tsararraki wadanda a kodayaushe suke samuwa ga matasa.
“Tabbas Arewa ta yi rashin wani babban jigo, amma matasan sun rasa jagora, majiyyaci, tarihin rayuwa da kuma sigar dukkan kyawawan halaye da ya kamata matasan Arewa su yi kokarin cimma.
“Muna rokon Allah Madaukakin Sarki da Ya yi watsi da gazawarsa, Ya gafarta masa kurakuransa tare da tausasawa, ya shigar da shi Aljanna, ya kuma baiwa iyalansa hakurin jure rashin,” in ji Suleiman.