Kun bani Kunya Sosai — Buhari ya gayawa Hukumomin tsaro kan harin Kuje
Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya bayyana rashin jindaɗin sa na yadda ɓangaren bayanan sirri suka kasa komai, biyo bayan harin da aka kai a Gidan Gyaran Aƙidu na Kuje.
Bayan ya duba harin a ranar Laraba, Shugaban yace “kun bani Kunya ɓangaren bayanan sirri na Kasa. Ta yaya Ƴan Ta’adda suka shirya, suka samu makamai, suka kai hari wajen jami’an tsaro, kuma su tafi.
KARANTA WANNAN LABARIN: APC ce Zata lashe Zaɓen Gwamnan Osun — Inji Buhari
A cewar Mai Magana da Yawun Shugaban Ƙasa Garba Shehu, “jim kaɗan bayan Shugaban Ƙasa ta ziyarci wurin, Babban Sakataren Ma’aikatar Cikin Gida Dr. Shu’aib Mohammed Lamido Belgore ya yi mashi jawabi, da Kwanturola Janar Haliru Nababa, inda suka nuna mashi wuraren da aka kai hari, da kuma yadda suka ƙone ofisoshi, yana mai kara da cewa, Maharan sun kai hari inda ƴan Ta’addan Boko Haram suke tsare.
“Shugaban ya bayyana takaici na yadda bayan harin ba’a gano koda Ɗan Boko Haram ɗaya ba, amma an gano bayanai.
Shehu a cikin wata sanarwa daya fitar bayan ziyarar, Shugaban Ƙasa kamar kowane Ɗan Najeriya ya bayyana tsoro na yadda aka kai hari. Ta yaya ɓangaren tsaron Gidan Yarin ya kasa kare harin. Fursunoni nawa ne? Jami’ai nawa ke gare ku masu aiki? Nawa ne keda makamai? Ina masu tsaro a saman gidan? Mi suka yi? Kamara na aiki?
Shugaban Kasar an sanar dashi cewa Jami’an tsaro sun kamo mutane 350 a yayinda mutane 450 an rasa inda suke, ana cigaba da ƙoƙari domin sake kamo sauran.
Shehu yace Shugaba Buhari ya samu rakiyar Boss Mustapha, Sakataren Gwamnatin Jaha, Farfesa Ibrahim Gambari, Shugaban Ma’aikata, yace bayan ziyarar ana saran za’a samu rahoto akan lamarin.
A lokacin da yake jawabi akan ziyarar sa zuwa Dakar, Senegal, ya bayyana cewa Gwamnati bata daina aiki don ƙasa na fuskantar barazanar ƴan ta’adda.