Kungiyar gwamnonin Nijeriya, NGF, ta yi tir da Allah-wadai da kisan manoman shinkafa fiye da 110 da ‘yan ta’addan Boko Haram ta yi a garin Zabarmari dake karamar hukumar Jere a jihar Borno a ranar Asabar.
Kungiyar a cikin sanarwar da ta fitar ta hannun shugabanta kuma gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi, a ranar Lahadi a Abuja, ta bayyana harin a matsayin abin Allah-wadai.