Kungiyar da ke karkashin Kungiyan Hausawan Nigeria ta bayar da tallafin kayan agaji ga ‘yan gudun hijira a jihar Zamfara.
‘Yan gudun hijirar sun kasance wadanda harin ‘yan bindiga ya shafa wanda ya tilasta musu barin gidajen kakanninsu
Shugaban kungiyar Abdullahi Abdullahi ya ce tallafin ya zama dole duba da irin wahalhalun da IPD ke fuskanta
“Tare da tawali’u da kuma kudurinmu na cigaba da bayar da tallafi ga marasa galihu da wadanda rashin tsaro ya rutsa da su a yau domin kai ziyarar agaji ga mutanen da suka koma gudun hijira a kasarsu.”
“Muna yi muku addu’a da gaske Allah ya dawo da ku cikin gaggawa don fara rayuwa ta hanya mafi kyau”.
Abdullahi ya lura da cewa ‘ya’yan kungiyar na ciki da wajen kasar nan ne ke ba da gudummawar kayayyakin da aka bayar
“Mun jawo hankalin mambobinmu kan abun da ke faruwa a Arewacin Najeriya kuma sun yi kira sun aika da gudunmawar su, shi ya sa muka zo nan domin cika alkawarin da muka dauka.” Inji Abdullahi