Yan Kungiyar IPOB sun yi ikirarin cewa tsohon Gwamnan Jihar Imo, Rochas Okorocha, ya yi yunkurin shiga kungiyar ta IPOB, sau da dama, amma shugabancinta ya ki amincewa da shi.
Don haka kungiyar ta gargade shi da ya daina amfani da su wajen siyasa domin yin hakan zai kai shi ga “barna a siyasa”.
A wata sanarwa da ya fitar a jiya Litinin, Sakataren Yada Labarai na kungiyar IPOB, Emma Powerful, ya ce dole ne ‘yan Najeriya su kula da Okorocha, kamar yadda ta yi zargin cewa tsohon gwamnan da makarrabansa ne ke kai hare-hare da kashe-kashe da sace-sace da ake yi a jihar Imo.
Don haka ta kalubalanci Okorocha da ya nemi Gwamnatin Tarayya ta gudanar da zaben raba gardama kan Biyafara idan har suna son a gwada farin jini.
Ta ce Gwamnatin Tarayya ba za ta samu kuri’ar “a’a” ba a zaben raba gardama domin a cewarta, daukacin al’ummar Kudu-maso-Gabas na son samun ‘yancin kai daga Najeriya kuma babu wani abin tsoro da zai iya hana hakan.