Kungiyar Miyetti Allah ta ƙaddamar da Rundunar ƴan Sa Kai mai Mutane 1,144 domin yakar Ƴan Ta’adda A Nasarawa
Kungiyar al’adun Fulani ta Miyetti Allah Kautal Hore ta kaddamar da wata kungiyar ‘yan banga mai dakaru 1,144 don yaki da matsalar garkuwa da mutane da satar shanu a ƙananan hukumomi 13 da ke cikin Jihar Nasarawa.
Shugaban Miyetti Allah na ƙasa Mista Abdullahi Bello Bodejo ne ya bayyana haka a lokacin da yake ƙaddamar da Dakarun a garin Lafiya.
KARANTA NAN:NiMet ta yi hasashen samun hasken rana da hazo na kwanaki 3
Bodejo ya gargadi ‘yan banga na sa kai da su hada kai da rundunar ‘yan sanda, da Sojojin sama da sauran jami’an tsaro yayin gudanar da ayyukansu.
Ya ce “Kungiyar ‘yan banga makiyaya ba shiri ba ne kawai; face
wata alama ce ta sadaukar da kai domin samar da ayyukan yi ga tattalin arziki da kuma yaki da barayin shanu masu garkuwa da Mutane, da kuma yaƙar yunwa da fatara a Jihar.
A wani labarin kuma:Duk da tsarin haɗa SIM da NIN, har yanzu Rashin Tsaro na ƙara Ta’azzara
Duk da tsarin haɗa SIM da NIN, har yanzu Rashin Tsaro na ƙara Ta’azzara
Matsalar tsaro a sassa daban-daban na Najeriya na ci gaba da tabarbarewa duk kuwa da tsarin haɗa SIM da katin ɗan ƙasa NIN da aka ɓullo da shi a ranar 16 ga watan Disambar shekarar 2020 kamar yadda wani rahoto ya bayyana a Ranar Lahadi.
Gwamnatin Tarayya ta baiwa ‘yan Najeriya tabbacin cewa tsarin haɗa SIM da NIN zai baiwa hukumomin tsaro damar bin diddigin masu aikata laifuka.
A ranar 6 ga watan Mayu, 2021, tsohon Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa, daidaita NIN da SIM a duk faɗin ƙasar yana da matukar muhimmanci wajen samar da tsarin zamani wajen yaƙar rashin tsaro.
Buhari a lokacin da yake ƙaddamar da tsarin inganta harkokin ‘yan kasa a fannin sadarwa na Najeriya da kuma sake fasalin tsarin tantance SIM da katin ɗan kasa a Abuja a wancan lokacin ya bukaci ‘yan Najeriya da su baiwa tsarin haɗin kai domin cimma manufar shirin.
Hukumar NIN za ta toshe wani ɓangare daga cikin raunin da ke tattare da tsarin tsaron Kasar mu. Za mu iya ganowa da sanin halin ‘yan Najeriya cikin sauki. Za mu iya gano mutane cikin sauki har da ‘yan damfara,” inji shi.
Buhari ya yi nuni da cewa, aikin zai tallafa wa ƙoƙarin inganta tsaro da bunƙasa tattalin arziki a kasar.
NIN ita ce tushen samar da bayanai na Zamani dangane da Dukan ‘yan Najeriya, da ma baƙi mazauna waɗanda doka ta baiwa damar zama. Muna sa ran kowa zai samu wannan lambar ta musamman, hakan Zai ba da damar yin amfani da ayyukan gwamnati, wanda hakan zai ba mu damar yin amfani da ƴan albarkatun da muke da su ta hanyar da ta dace.
shugaban kasa ya tabbatar.
Sai dai fiye da shekaru uku bayan bijiro da tsarin haɗa SIM da NIN ɗin, amma ‘yan fashi da sauran masu laifi sun yi garkuwa da dubban mutane a sassa daban-daban na kasar nan.
Kusan a dukkan lokuta masu laifin sukan zanta ne ta layin wayar hannu da iyalan waɗanda abin ya shafa domin biyan maƙudan kuɗaɗe a matsayin kuɗin fansa.
Wasu bayanai da Wakilin mu ya tattara a ranar Lahadin bisa la’akari da rahotannin kafafen yaɗa labarai sun nuna cewa tsakanin 16 ga Disamba 2020 zuwa Janairun bana an yi garkuwa da mutane sama 12,586 a faɗin Jihohi da Babban Birnin Tarayya (FCT).
A cikin lokacin da ake bitar an ba da rahoton cewa ‘yan bindiga sun kashe jimillar mutane 10,012 a faɗin kasar. 837 a cikin shekarar 2020; da
4,169 a cikin shekarar 2021; sai
2,310 a cikin shekarar 2022; da
2,586 a cikin shekarar 2023 da kuma 110 a cikin Janairu 2024.