Duk da tsarin haɗa SIM da NIN, har yanzu Rashin Tsaro na ƙara Ta’azzara
Matsalar tsaro a sassa daban-daban na Najeriya na ci gaba da tabarbarewa duk kuwa da tsarin haɗa SIM da katin ɗan ƙasa NIN da aka ɓullo da shi a ranar 16 ga watan Disambar shekarar 2020 kamar yadda wani rahoto ya bayyana a Ranar Lahadi.
Gwamnatin Tarayya ta baiwa ‘yan Najeriya tabbacin cewa tsarin haɗa SIM da NIN zai baiwa hukumomin tsaro damar bin diddigin masu aikata laifuka.
A ranar 6 ga watan Mayu, 2021, tsohon Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa, daidaita NIN da SIM a duk faɗin ƙasar yana da matukar muhimmanci wajen samar da tsarin zamani wajen yaƙar rashin tsaro.
Buhari a lokacin da yake ƙaddamar da tsarin inganta harkokin ‘yan kasa a fannin sadarwa na Najeriya da kuma sake fasalin tsarin tantance SIM da katin ɗan kasa a Abuja a wancan lokacin ya bukaci ‘yan Najeriya da su baiwa tsarin haɗin kai domin cimma manufar shirin.
KARANTA NAN:Ƴan sanda sun dakile yunkurin garkuwa da mutane sau 2, sun kuɓutar da mutane 5 a Katsina
Hukumar NIN za ta toshe wani ɓangare daga cikin raunin da ke tattare da tsarin tsaron Kasar mu. Za mu iya ganowa da sanin halin ‘yan Najeriya cikin sauki. Za mu iya gano mutane cikin sauki har da ‘yan damfara,” inji shi.
Buhari ya yi nuni da cewa, aikin zai tallafa wa ƙoƙarin inganta tsaro da bunƙasa tattalin arziki a kasar.
NIN ita ce tushen samar da bayanai na Zamani dangane da Dukan ‘yan Najeriya, da ma baƙi mazauna waɗanda doka ta baiwa damar zama. Muna sa ran kowa zai samu wannan lambar ta musamman, hakan Zai ba da damar yin amfani da ayyukan gwamnati, wanda hakan zai ba mu damar yin amfani da ƴan albarkatun da muke da su ta hanyar da ta dace.
shugaban kasa ya tabbatar.
Sai dai fiye da shekaru uku bayan bijiro da tsarin haɗa SIM da NIN ɗin, amma ‘yan fashi da sauran masu laifi sun yi garkuwa da dubban mutane a sassa daban-daban na kasar nan.
Kusan a dukkan lokuta masu laifin sukan zanta ne ta layin wayar hannu da iyalan waɗanda abin ya shafa domin biyan maƙudan kuɗaɗe a matsayin kuɗin fansa.
Wasu bayanai da Wakilin mu ya tattara a ranar Lahadin bisa la’akari da rahotannin kafafen yaɗa labarai sun nuna cewa tsakanin 16 ga Disamba 2020 zuwa Janairun bana an yi garkuwa da mutane sama 12,586 a faɗin Jihohi da Babban Birnin Tarayya (FCT).
A cikin lokacin da ake bitar an ba da rahoton cewa ‘yan bindiga sun kashe jimillar mutane 10,012 a faɗin kasar. 837 a cikin shekarar 2020; da
4,169 a cikin shekarar 2021; sai
2,310 a cikin shekarar 2022; da
2,586 a cikin shekarar 2023 da kuma 110 a cikin Janairu 2024.
Majiyoyi daga Hukumar Kula da Shaidar katin ɗan Ƙasa (NIMC) da ta zanta da Wakilin mu ta ce, adadin masu amfani da layin waya da aka haɗa da katin ɗan ƙasa a Najeriya ya kai 221,769 883.
Hukumar Sadarwa (NCC) a watan Satumbar shekarar da ta gabata ta yi nuni da cewa har yanzu kusan layukan waya Miliyan 12 ne ake aiki da su ba tare da an haɗa su da NIN.
Watakila adadin ya zarce miliyan 13 a wannan watan na Janairu domin an sayar da SIM da yawa tsakanin watan Nuwamba zuwa yanzu,” wata majiya mai tushe ta NCC ta ce.
Tsohon Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki na Zamani Isa Pantami a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter a ranar Lahadin da ta gabata ya ce gazawar da hukumomin tsaro suka yi na yin amfani da bayanan da aka samar daga SIM-NIN ya karfafawa masu garkuwa da mutane da sauran laifuka.
Tun da farko a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Tuwita ya bayyana cewa wani abokinsa ya tara Naira miliyan 50 a matsayin gudummawar kuɗin fansa Naira miliyan 100 da masu garkuwa da wasu mata shida da mahaifinsu suka nema a Abuja.
Ya ce tsarin haɗa SIM da NIN ba ita ce matsalar ba, illa rashin amfani da shi ne ga hukumomin da ya kamata su yi.
Rashin yin amfani da shi shine babbar matsalar ba manufar ba, A lokacin da nake ofis na san lokuta uku da aka yi amfani da manufar kuma ta haifar da nasara.
Wani kwararre a fannin tsaro Chukwuma Ume a wata tattaunawa da ya yi da ɗaya daga cikin wakilanmu ya ce jami’an tsaro na da damar samun NIN da kuma fasahar gano masu aikata laifuka.
Sai dai ya ce ‘yan ta’addan suna da kaifin basira, inda suke amfani da katin SIM na waɗanda su kayi garkuwa da su wajen yin waya da ƴan’uwansu domin neman kuɗin fansa.
Ya kuma bayar da misali da yadda jami’an hukumar ke gudanar da ayyuka masu tsauri wadanda a cewar sa suka yanke hukunce-hukunce wajen gudanar da ayyukansu.
Abun shine jami’an tsaro suna da damar shiga manhajar NIN kuma ina so in yi imani cewa suna da fasahar da za su yi amfani da su don ganowa, amma abin da na sani shi ne cewa da zarar waɗannan masu laifin sun aikata, to sai su koma daji, kuma da zarar sun koma daji, to shikenan, za su cigaba da cin karen su ba babbaka.