Kungiyar iyaye da malaman jami’o’i ta kasa ta nemi gwamnatin tarayya da ta kawo karshen yajin aikin da kungiyar malaman jami’o’i take yi.
Kungiyar ta kuma bayar da shawarar biyan N10,000 a kowane wata ga kowane iyayen Dalibin jami’a, don taimakawa gwamnati wajen samar da karin kudade ga jami’o’in.
Jami’in hulda da jama’a na kungiyar NAPTAN, Dokta Ademola Ekundayo, ya bayyana hakan yayin wata tattaunawa da manema labarai a ranar Talata.
KARANTA ANAN: Edo PDP: An Mayar Da Martani Yayin Da Mambobin Ke Jiran Kotun Koli
Ekundayo, wanda ya koka da yadda ake ci gaba da rufe jami’o’in kasar nan, ya ce iyaye sun gama kaiwa bango kan rashin jituwar da ke tsakanin Gwamnatin Tarayya da ASUU.
Ya ce, “Mun mika takarda ga ofishin ministan ilimi, muna neman a saurare mu inda muke fatan tattauna wata shawara.
“Muna ba da shawarar bayar da Naira 10,000 don tallafawa gwamnatin tarayya, wajen biyan bukatun kungiyar ASUUn.
Wannan zai zama tamu gudunmawar baya ga sauran kudaden da doka ta kayyade wajen samarwa a natsayin karin kudade ga jami’o’i.
“Ana iya kiransa harajin tallafin iyaye ga jami’o’i, don mun kasance a matakin karshe wajen zuwa wuya kan wannan yajin aiki da ASUU take yi.
Muna rokon kungiyar ASUU da gwamnatin tarayya da su gaggauta warware taƙaddamar dake tsakanin su.”
A wani labarin kuma: Jami’an ‘Yan Sanda Ba Sa Bin Wani Albashi – Kwamishinan ‘Yan Sandan Kwara
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kwara, CP Tuesday Assayomo, ya ce jami’an ‘yan sanda ba sa bin kowane dan sanda ko mace albashi, haka kuma rundunar ba ta biyan su wani albashin na musamman.
Assayomo ya bayyana haka ne a yayin da yake mayar da martani ga wata zanga-zangar da wasu ’yan sanda na musamman suka yi wanda ya haifar da cunkoson ababen hawa a babbar hanyar Ahmadu Bello da ke Ilorin, babban birnin jihar, bisa zargin rashin biyan albashi.