Kungiyar Kafefen Yada labarai ta Arewacin Nigeria (NBMOA), ta Gudanar da taron liyafar dare, ga Shugabannin wadannan kafafen yada labarai.
Taron dai ya gudana a Daren Jiya, a Dakin taro na Dabo TV dake Kan titin zuwa Jami’ar Bayero Kano, wanda kuma bayan Liyafar, an karrama wasu daga cikin Yan kungiyar sakamakon irin gudunmawar da suka bayar wajen ci gaban harkar yada labarai.
Jamaa da dama ne suka halarci wajen Liyafar, cikin su har da Hadimi ga Shugaban Kasa Bashir Ahmad, da sauran manyan Mutane masu rike da madafun iko da wadanda suka gabata.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa daga cikin wadanda aka karrama, sun Hadar da Fatima Amin, Shugabar Gidan Talabijin ta Zamani, Alhaji Farouq Dalhatu tsohon Shugaban rukunin gidajen Rediyo na Freedom, da Asma’u Sadik Shugabar sashin shirye shirye ta Dala FM da sauran su.