Gwamnan Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya ce ƙofar sulhu a buɗe take tsakaninsu da ɓangaren Sanata Ibrahim Shekarau, Wanda akewa lakabi da G7.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a Jiya Lahadi, yayin Taron murnar samun nasara a kotun daukaka Kara dake Abuja, Wanda kuma Taron ya gudana ne a Dakin taro na Coronation dake Gidan Gwamnati, Yana Mai cewa yanzu lokaci ne, na tafiya tare da mayar da hankali ga ci gaban Jam’iyyar APC.
Gwamnan na Kano, ya ce “Muna rokon ‘yan uwanmu a zo a hada a hannu gaba ki daya don a yi wannan tafiya tare, sannan kuma ina so na sanar da ‘yan jam’iyya cewa a daura damara don yanzu za a shiga gwagwarmayar zaben 2023, dake tafe”.
Dr Abdullahi Umar Ganduje, ya ce duk da G7 sun dauki hanyar daukaka kara zuwa kotun koli hakan ma dimokradiyya ce, kuma hakan ba zai hana azo a dai-daita a ci gaba da tafiya tare ba.