Babban Bankin Najeriya ya gargaɗi ƴan Najeriya dasu zama masu kula akan manhajoji da shafuna na bogi na eNaira.
Majiyar Jaridar Dimokuraɗiyya ta ruwaito cewar, Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya kaɗɗamar da kuɗaɗen Babban Bankin Najeriya na yanar gizo da ake kira da eNaira a ranar Litinin.
Domin samun eNaira, masu amfani zasu iya sauke manhajar mai suna ‘speed wallet’ wanda zai baiwa mutane damar gudanar da harkokin su na kuɗi cikin sauƙi.
KARANTA WANNAN LABARIN: Kwamitin Majalisar Dattawa Ya Amince Da Biyan Naira 1,000 Don Ciyar Da Fursunoni A Kullum
A cikin wata sanarwa da Babban Bankin Najeriya ya fitar a ranar Laraba, Babban Bankin yace tuni wasu sun fara damfarar al’umma.
“Biyo bayan kaɗɗamar da eNaira a ranar Litinin 25 ga watan Oktoba na Shekarar 2021, hankalin Babban Bankin Najeriya yakai ga wasu ɓata gari, masu gudanar da ayyuka ba bisa ƙa’ida ba, wanda suke cutar al’umma a shafin Twitter mai suna @enaira_cbdc cewa na Bankin.
“Tuni masu damfara sun ƙirƙiri shafuna tare da tura saƙonni akan eNaira da manufar cutar al’umma, inda suke cewa ya danganci Babban Bankin Najeriya, daga cikin ƙaryar da suke yi ya haɗa da cewa za’a rarraba Naira biliyan 50 akan kuɗaɗen eNaira.
Al’ummar Najeriya zasu iya neman sahihan bayanai ta hanyar ziyartar www.enaira.gov.ng ko kuma su kira 08069362472 ko kuma su ziyarci reshen Babban Bankin Najeriya dake kusa dasu.
“Domin neman bayanai sahihan shafunan eNaira sune www.facebook.com/myenaira; www.instagram.com/myenaira da kuma www.youtube.com/myenaira.
Za’a iya kai ƙorafi akan ƴan damfara ga Babban Bankin Najeriya ta hanyar tura saƙo akan helpdesk@enaira.gov.ng ko kuma ga Hukumomi da lamarin ya shafa