Mazauna jihar katsina na cike da fargaba, bayan barkewar cutar Kwalara, da ta yi sanadiyar mutuwar akalla Mutum 60, a wasu yankuna dake fadin jihar.
Kwamishinan kula da kiwon lafiya na jihar, Yakubu Danja ne ya bayyana hakan a taron shekara shekara na shekarar 2021, daya gudana a sakatariyar Ma’aikatar dake katsina.
Ya ce, tuni aka siyo magunguna kuma aka raba su ga daukacin asibitoci dake jihar, domin dakile yaduwar cutar a jihar.
Danja ya kara da cewa, tuni jami’an kiwon lafiya suka fara wani bincike na musamman, a daukacin kananan hukumomi 34 dake fadin jihar, domin wayar dakan al’uma da kuma dakile yaduwar cutar.
Ya kara da cewa, “Yanzu haka mun sami rahotannin mullar cutar guda 1,400, inda sama da Mutum 60 ne su ka mutu sanadiyar cutar” a cewar shi.
KARANTA WANNAN LABARIN: Jihohin 20 da Majalissar Dattijai ta bukaci a kirkira a Nigeria
Kazalika Kwamishinan ya kuma shawarci al’umar jihar, da su Kula da tsabtar Muhalli su, yawaita wanke hannu, kula da abinci, wanke kayan marmari kafin aci, Shan ruwa Mai tsafta, da kuma tabbatar da an dafa kayan abinci kamar yadda ya dace.
Ya kuma bukaci masu saida abinci akan hanya, da su dunga rufe kayayyakin su, domin kauce wa kudaje.
Majiyar jaridar Dimokuradiyya ta ruwaito mana cewar, al’umar wasu yankuna a jihar ta Katsina, na cikin fargaba sakamakon barkewar cutar.