Gwamann jihar Oyo ya ayyana ranar Talata 10 ga watan Ogustan shekarar 2021 a matsayin ranar hutu ga Ma’aikatar, domin burnar zagayowar sabuwar shekarar Musulunci na 1 ga watan Muharram shekarar 1443 AH.
Bayanin hakan na kunshe ne, a cikin wata sanarrwa da ta fito daga ofishin sakataran gwamnatin jihar, inda kuma ya rabawa manema labarai a garin Ibadan.
Sanarwar dauke da sahannun sakataran Gwamnatin jihar Mrs Olubamiwo Adeosin, ya mata lakabi da ” Ayyana ranar hutu ga Ma’aikatan jihar, don murnar Hijirah 1443 AH.”
KARANTA WANNAN LABARIN: Cutar Kwalara ta kashe mutum 60 a jihar Katsina
Kazalika sanarwar ta nuna yadda Gwamnan ke cewa, ” Gwamna Seyi Makinde, na cike da farinciki kamar kowa, da kuma tabbatar da yi wa jihar Oyo addu’ar fatan samun zaman lafiya, hadin Kai l, da kuma ci gaba da dorewar jihar, dama kasa baki daya” inji sanarwar.
A wani labarin Kuma.
A halin yanzu Rundunar Sojin Nigeria ta amshi mambobin Yan Boko Haram/ISWAP guda 605 Wanda suka ajiye makaman su, tare da mika wuya, kamar yadda PRNigeria ta ruwaito.
Haka Zalika, kimanin mutane 229 Wanda daga cikin su mata ne da Kananan Yara, tuni aka mika su ga Gwamnatin Jahar Borno.
A makonni da suka gabata, da yawa daga cikin Mayakan Boko Haram ne da iyalansu, suka bayyana cewa sun ajiye mummunan gangamin da suke yi na Jihadi, tare da mika wuyan su ga Rundunar Sojin Nigeria.
Wani daga cikin Sojin da aka yi yakin dashi, ya bayyanawa Majiyar mu cewa, ajiye makamai da tubabbun Yan ta’addan sukayi da iyalansu ya yi dai-dai da dokar duniya, daya baiwa Yan ta’adda dama ajiye makaman su.
Acewar Babban Jami’in , wasu daga cikin Mayakan na Boko Haram suna jin tsoron cewa, za’a iya kashe su, idan suka mika wuya, amma sai sukayi mamaki na yadda aka karbe su, dasu da iyalansu da iyayensu.
Jami’in yace, da yawansu iyayen su da Matayen su, ke basu kwarin gwuiwar cewa zasu tsaya masu idan suka ajiye makaman su.