By Abbas Yakubu Yaura
Hukumomin Kwalejin Fasaha ta Tarayya, Ede dake Jihar Osun, sun dakatar da gudanar da zaben kungiyar dalibai har sai an samu kwanciyar hankali biyo bayan tashin hankalin da ya barke tsakanin kungiyoyi biyu.
DUBA WANNAN LABARIN: Mutane Takwas Sun Mutu A Hatsarin Mota A Jihar Legas
Hakan na kunshe ne a cikin wata takarda mai dauke da sa hannun shugaban kula da harkokin dalibai, Dakta Oluyemi Omotosho (Jnr), inda hukumar kula da makarantar ta bayyana cewa akwai bukatar a dakatar da zaben kungiyar dalibai saboda tashe-tashen hankula da yakin neman zabe ya haifar.
Hukumar kula da makarantar ta bayyana cewa, an yanke hukuncin dakatar da zaben ne bayan ta yi nazari kan yanayin tsaro a harabar makarantar da kuma yadda lamarin ya shafi al’ummar Ede.
Sanarwar ta ce, “Lokacin da kungiyar ISEC ta dage haramcin siyasa a ranar 21 ga watan Maris, 2022, kowa ya yi fatan za a gudanar da zabe ba tare da tashin hankali ba har sai da ‘yan takarar shugabannin kungiyar daliban biyu, Akeem Kabiru Olawale (Kaybright) da Edward Ayodeji Michael (Edward) suka fara gangamin yakin neman zaben na ranar 24 ga watan Maris, 2022.
“Kungiyoyin biyu sun yi arangama kuma rikici ya barke, wanda ya yi sanadin jikkata dalibai da dama. An kama wani mai goyon bayan ‘yan takarar bayan ya yi amfani da adda wajen raunata wani dalibi sannan kuma an kama wani dalibi da bindiga.
“Hukumomin sun duba kalubalen tsaro a harabar kwalejin fasaha ta tarayya da kuma al’ummar Ede inda suka dauki matakai kamar haka;
“An dakatar da zaben SUL na 2021/2022 har sai lokacin da kalubalen tsaro ya inganta don hana asarar rayuka da dukiyoyi.
“Ya kamata a binciki daliban da aka kama wadanda suke da hannu a cikin aikata laifuka.
“An umurci dalibai da su fara shirye-shiryen jarrabawar zangon karatu na biyu wanda zai fara daga ranar 4 ga watan Afrilu, 2022.”
A halin da ake ciki, shugaban kungiyar dalibai mai ci, Adekunle Jimoh, ya bayyana cewa hukumar ba ta hada da kungiyar ba a lokacin da aka yanke shawarar dakatar da zaben.
Ya bayyana cewa zai gana da mahukuntan makarantar a ranar Litinin domin ganin an dage dakatarwar, yayin da ya ba da shawarar cewa a hana masu neman shiga rikicin.
“Zan gana da hukumar a ranar Litinin. Hukumar ba za ta iya ba saboda abin da ya faru ya hana zaben. Za mu yi zaben mu.
“Maimakon a dakatar da zaben, ya kamata a hana masu neman takara biyu da ke da hannu a rikicin shiga zaben,” in ji Jimoh.