Kwamishinan Ma’aikata da batutuwan tsaro na Jihar Sakkwato, Kanar Garba Moyi mai ritaya, ya fice daga jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyar APC.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa dauke da sa hannun Malam Bashar Abubakar, mataimaki na musamman kan sabbin kafafen yada labarai, ga Sanatan sokoto ta Arewa Aliyu Wamakko ranar Lahadin nan a Abuja.
Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya ruwaito cewa, hakan na zuwa ne sa’o’i 24 bayan ficewar shugaban karamar hukumar Tangaza, Alhaji Salihu Kalanjeni daga jam’iyyar PDP zuwa APC.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Kalanjeni ya sauya sheka ne tare da wasu kansiloli guda takwas da kuma tsofaffin kansiloli guda biyu.
Ya ce shugaban jam’iyyar na jihar, Wamakko ne ya tarbe Moyi a cikin jam’iyyar APC.
KARANTA WANNAN: https://dimokuradiyya.com.ng/da-dumi-dumi-tsohon-shugaban-jamiar-lasu-hussein-ya-rasu-yana-da-shekaru-75/
Abubakar ya ce kwamishinan ya kuma bayyana ficewarsa daga jam’iyyar PDP mai mulki da kuma majalisar zartarwa ta jihar.
Da yake karbar Moyi, Wamakko ya bukace shi da ya yi aiki tukuru wajen ganin jam’iyyar APC ta samu nasarar lashe zaben Sanatan Sokoto ta Gabas da ma jihar baki daya a babban zaben 2023 mai zuwa.
(NAN)