Kwamishinan ƴan Sanda ya ziyarci tashar Watsa Labarai, ya nemi afuwa akan abinda ya faru
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Abia, Mista Kenechukwu Onwuemelie ya ziyarci hedkwatar kamfanin watsa labarai na All Breaking News (ABN) da ke kan titin Azikiwe a Umuahia domin duba abinda ya faru a ofishin.
Idan ba a manta ba a ranar Talata ne wasu ‘yan sanda suka kutsa kai a daƙin watsa labarai na tashar domin kama wani mutum da suke nema.
Sai dai Kwamishinan wanda ya ziyarci ofishin ABN ɗin tare da wasu manyan Jami’an ‘yan sanda ya nemi afuwar Ma’aikatan tashar, inda ya kara da cewa an sasanta tsakanin bangarorin biyu bayan tattaunawa tsakanin Kwamishinan da Daraktan tashar ta ABN.
Wata sanarwar da kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar Abia Maureen Chinaka ya sanya wa hannu a madadin Kwamishinan ƴan Sandan ta ce, binciken farko da aka gudanar kan lamarin ya nuna cewa jami’an ‘yan sandan da suka yi kamen sun gudanar da kamen ne ba bisa ka’ida ba.
KARANTA NAN:“Dole ne a bi ƙa’ida wajen kama wanda ake zargi” – Shugaban EFCC ga Jami’an hukumar
Sanarwar ta ƙara da cewa “Wannan saboda duk da cewa babu wata doka da ta hana jami’in ‘yan sanda yin kame a kowane irin ɗakin taro, hujjojin da ke tattare da lamarin da jami’an ‘yan sandan ke gudanar da bincike ba su sa a yi irin wannan aiki ba.
Kwamishinan ‘yan sandan Jihar Abia ya ziyarci gidan talabijin na ABN TV/Radio a ranar 17/1/24 inda ya Jagoranci a nan take ya tattaunawa da Daraktan gidan talabijin na ABN TV/Radio tare da ba da hakuri kan abinda jami’an suka yi cikin aminci da lumana.
Sai dai jami’an da su kayi kamen sun aikata laifi, kuma an fara bincikensu akan lamari a yau, idan aka same su da laifi ta za a hukunta su.
Rundunar ‘yan sandan Jihar Abia ta duƙufa wajen ganin ta ci gaba da bin doka da oda da kyautata alaka da jama’a da kuma abokantaka kamar yadda babban sufeto Janar na ‘yan sanda IGP Kayode Ebetokun PhD NPM ya bayyana.